Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaushe 'yan siyasar Amurka za su daina dorawa wasu laifi?
2020-06-26 19:37:54        cri

Kwanan baya shugaban kasar Amurka ya gabatar da jawabi yayin gangamin yakin neman zaben shugabancin kasa, inda ya yi amfani da kalmomin nuna wariyar launin fata wato Kung Flu, yayin da shi kuma Navarro, darektan ofishin tsara manufar cinikayya da sana'ar kere-kere na White House ya yada jita-jitar cewa, kasar Sin ce ta kirkiri kwayar cutar COVID-19, har fadar White House ta bayyana cewa, za ta binciki kuskuren da cibiyar CDC ta kasar ta yi yayin da take dakile annobar, an lura cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, 'yan siyasar Amurka suna daukar matakan dora laifi ga wasu, wannan ya sa jama'a ke nuna damuwa kan yaushe ne za su dawo hayyacinsu?

Jaridar The Washington Post ta wallafa rahotanni da dama, inda a ciki ta sha sukar gwamnatin Amurka cewa, tana ci gaba da dora laifi domin neman karin goyon bayan Amurka a babban zaben dake tafe.

Amma ba zai yiyu ba matakan da suka dauka su boye hakikanin abubuwan da suke faruwa wato gazawar gwamnatin Amurka ta dakile annobar, da ma farfado da tattalin arzikin kasar.

A jiya Alhamis 25 ga wata, darektan cibiyar CDC ta Amurka Robert Redfield ya yi hasashe cewa, kila hakikanin adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ya kai kusan miliyan 25.

A halin da ake ciki yanzu, Amurka tana cikin mawuyacin yanayi wajen dakile annobar, a sanadin haka, 'yan kasar da yawansu ya kai fiye da miliyan 40 sun rasa aikin yi, har ma bankin duniya ya yi hasashe cewa, tattalin arzikin Amurka zai ragu da kaso 6.1 bisa dari a bana, kana asusun IMF ya yi hasashe cewa, tattalin arzikin kasar zai ragu da kaso 8 bisa dari.

Abun bakin ciki shi ne, yayin da 'yan siyasar Amurka suke ci gaba da dora laifi kan wasu, a hannu guda kuma, 'yan kasar suna ci gaba da rasa rayuka, kwanan baya mujallar The Atlantic ta Amurka ta wallafa wani rahoto, inda ta yi kashedi cewa, adadin mutanen da za su kamu da cutar zai karu, idan gwamnatin Amurka ba ta dauki matakan da suka dace ba, to tabbas ne al'ummun kasar za su shiga halin ha'ula'i da ba zai misaltu ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China