Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kada a bata sunan jihar Xinjiang ta fuskar yaki da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi
2020-06-22 14:36:31        cri

Kwanan baya, kasar Amurka ta sa hannu kan daftarin dokar kare hakkin dan Adam ta Uygur a shekarar 2020 don ya zama doka, inda ta shafa wa jihar Xinjiang ta kasar Sin bakin fenti ta fuskar kiyaye hakkin dan Adam, ta kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Abin da Amurka ta yi ya sake nuna mana cewa, Amurka maras sahihanci tana nuna fuska biyu wajen kiyaye hakkin dan Adam. Ainihin nufin Amurka shi ne tayar da hankali a kasar Sin da sunan hakkin dan Adam, da yunkurin hana ci gaban kasar Sin.

Jihar Xinjiang, babban fagen yaki ne na kasar Sin wajen yaki da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi. Batutuwan da suka shafi jihar ta Xinjiang ba su da nasaba da batun kare hakkin dan Adam, batun kabilu, batun addini, a'a, ba haka ba ne. sun danganta da yadda ake yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Mene ne ma'anar kiyaye hakkin dan Adam? Da farko dai a tabbatar da tsaron lafiyar mutane da kiwon lafiyarsu da kuma ci gabansu. Amma da sunan addini da kabilu ne 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi da 'yan a-ware suka kai dubban hare-hare masu ban tsoro a jihar Xinjiang daga shekarar 1990 zuwa karshen shekarar 2016, wadanda suka yi sanadin mutuwar dimbin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, tare da yin asarar dukiyoyi da yawa. Kamar yadda gwamnatin Nijeriya ta yi yaki da 'yan tawayen Boko Haram, gwamnatin kasar Sin tana daukar wajibabbun matakai na tabbatar da hakkin dan Adam ta hanyoyin yaki da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi a jihar ta Xinjiang da kuma kyautata zaman rayuwar mazauna jihar daga kabilu daban daban wadanda kuma suke bin addinai daban daban cikin 'yanci.

Ya zuwa yanzu dai matakan da kasar Sin ke dauka a jihar Xinjiang sun kyautata yanayin tsaro a jihar, inda ba a samu abkuwar harin ta'addanci a wurin cikin shekaru fiye da 3 da suka wuce ba. Mutane daga kabilu daban daban wadanda suke bin addinai daban daban suna jin dadin zamansu a jihar ta Xinjiang cikin kwanciyar hankali.

Da ganin yadda Amurka take keta hakkin dan Adam a gida, ya fi kyau ta yi tunani sosai kan abubuwan da ta yi tukuna. Kada ta soki sauran kasashe da sunan kare hakkin dan Adam, da kuma mayar da baki fari. In ba haka ba, za ta yi amai ta lashe a karshe. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China