Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai karin mutane 56 da suka kamu da cutar COVID-19 a Nijer cikin makon da ya gabata
2020-06-22 13:41:08        cri
A jiya Lahadi ne ma'aikatar kiwon lafiyar jamhuriyar Nijer, ta fidda rahoton cewa, cikin makon da ya gabata, gaba daya, an samu karin mutane 56 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19, kuma mutane 55 daga cikin adadin sun shiga da cutar ne daga kasashen ketare. Kana, mutane 26 sun warke daga cutar, yayin da mutum daya ya rasu sakamakon cutar.

Tun farkon gano mai dauke da cutar a kasar a ranar 19 ga watan Maris na bana, ya zuwa yanzu, jamhuriyar Nijer ta yi gwajin cutar COVID-19 kan mutane 6170, inda aka tabbatar da mutane 1036 sun kamu da cutar, kana, mutane 911 sun warke, yayin da mutane 67 suka rasa rayukansu sakamakon cutar COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China