Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi kira da a dawo da yara 'yan Tunisia da suka makale a sansanonin 'yan gudun hijira dake Syria da Libya
2020-06-22 11:17:39        cri

Wani jami'in kare hakkin dan Adam a Tunisia, ya yi kira da a dawo da yara 'yan Tunisia dake makale a sansanonin 'yan gudun hijira a Syria da Libya.

Kafar watsa labarai ta Tunis Afrique, ta rawaito Marouan Jedda, babban daraktan hukumar "Observatory of Rights and Freedoms" dake aiki a kasar Tunisia, na cewa akwai yara kanana 'yan asalin kasar har 110 da yanzu haka ke makale a sansanonin 'yan gudun hijira na kasar Syria, da wasu 36 a sansanonin kasar Libya.

Jami'in ya ce yaran sun rasa damar su ta cin moriyar ababen more rayuwa, ciki hadda abinci da kiwon lafiya, da kariya daga cututtuka ciki hadda cutar COVID-19.

Jedda ya kara da cewa, irin wadannan sansanoni na tattare da yiwuwar harbuwa da cututtuka, don haka ya jaddada muhimmancin dawo da su yankunan su na asali, wanda hakan hakkin su ne na halas. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China