Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang mai zaman karko da wadata ta fallasa karyar da 'yan siyasan Amurka suka yi
2020-06-20 20:20:40        cri

 

Kwanan baya, kasar Amurka ta sa hannu kan shirin dokar kare hakkin dan Adam na Uygur na shekara ta 2020, inda ta shafa wa kasar Sin bakin fenti kan halin hakkin dan Adam da jihar Xinjiang ta kasar ke ciki, da kuma manufofinta na gudanar da harkokin jihar, lamarin da ya sanya jama'ar kasar Sin, ciki har da al'ummar kabilu daban daban na jihar kimanin miliyan 25 yin fushi a kai, kuma al'ummar kasashen duniya masu rikon gaskiya sun soki matakin na Amurka.

Bisa kokarin da aka yi a jihar Xinjiang cikin dogon lokaci, musamman ma matakai masu amfani da aka dauka na yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi a 'yan shekarun da suka gabata, yanzu jihar na cikin wani sabon zamani na samun wadata da ci gaba.

A cikin shekaru 3 da wani abu da suka gabata, ba a samu harin ta'addanci a jihar ba. Kuma tun bayan babban taron wakilai na JKS karo na 18, matsakaicin kauwar GDP na jihar ya kai kaso 8.5 cikin 100 a ko wace shekara, yawan masu fama da talauci ya ragu daga kashi 19.4 cikin 100 a karshen shekarar 2013 zuwa kashi 1.24 cikin 100 a karshen shekarar 2019.

Yawan wuraren ibada dake jihar Xinjiang ya wuce dubu 28, kuma yawan malaman addini ya kai kusan dubu 30. Ko wadanne musulmai 530 na iya samun masallaci guda 1, adadin da ya zarce kasashen musulunci masu yawa.

 

 

Abubuwan shaida masu yawa sun nuna cewa, yanzu dai jihar Xinjiang na cikin wani lokaci mafi kyau na samun wadata da bunkasuwa a tarihi, an tabbatar da ikon jama'ar kabilu daban daban dake jihar a fannoni daban daban, ciki har da ikon rayuwa da na samu ci gaba.

Tun bayan karshen shekarar 2018, tawagogi sama da 70 da ke kunshe da mutane fiye da 1000 da suka fito daga kasashe 91 sun kai ziyara jihar Xinjiang, sun kuma bayyana cewa, abubuwan da suka gani, sun sha bamban da na wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka fada.

Jama'ar kabilu daban daban na jihar Xinjiang ne sun fi iya magana a kan batun Xinjiang. Kokarin da wasu ke yi na yada jita jita da bata sunan kasar Sin, ba zai rufe ainihin halin da jihar ke ciki ta fuskar samun ci gaba ba. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China