Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamian kasashen Afirka da dama sun yaba da jawabin da shugaban kasar Sin ya gabatar
2020-06-20 18:21:00        cri
Jami'an kasashen Afirka da dama sun yaba da jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron kolin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 da ya gudana kwanakin baya ta kafar bidiyo, inda suka bayyana cewa, a daidai lokacin da ake tsaka da yaki da cutar a fadin duniya, yadda aka gudanar da taron cikin nasara, ya shaida niyyar bangarorin biyu na hada kansu wajen yaki da cutar, lamarin da kuma ya samar da kuzari sosai ga kasa da kasa wajen karfafa hadin gwiwarsu ta fannin yaki da cutar.

Mashawarcin shugaban kasar Nijeriya kan harkokin yada labarai, Mr. Femi Adesina ya bayyana cewa, a jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya bayyana cewa, zumunta da aminci sun kara karfafa a tsakanin Sin da Afirka a yayin da suke yaki da cutar. Ya ce a ganinsa, abu ne da ke karfafa gwiwar al'umma, wanda kuma ya shaida cewa, kullum kasar Sin na mai da hankalinta a kan kasashen Afirka, da kuma walwalar al'ummarsu. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China