Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka tana fakewa da batun kare hakkin dan Adam wajen goyon-bayan 'yan ta'adda
2020-06-18 21:14:47        cri

A jiya Talata, Amurka ta zartas da shirin dokar kare hakkin dan Adam na Uygur na shekara ta 2020, inda ta yi yunkurin bata sunan kasar Sin bisa fakewa da batun hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, da kalubalantar manufofin gwamnatin kasar Sin kan jihar. Irin wannan abun da Amurka ta yi, ya sabawa dokoki gami da ka'idojin kasa da kasa, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, al'amarin da ya jawo babban takaici da adawar gwamnatin kasar.

A 'yan shekarun nan, akwai wasu 'yan siyasar Amurka wadanda suke yunkurin rura wutar rikici bisa hujjar batun Xinjiang, kuma makasudinsu a bayyane yake, wato kawo tashin-tashina a Xinjiang, da lalata hadin-kan al'ummomin kasar Sin, da kuma kawo cikas ga ci gaban kasar.

Sanin kowa ne, batun jihar Xinjiang, ba shi da alaka ko kadan da batun wata kabila, ko wani addini, ko kuma hakkin dan Adam, batu ne da ya shafi yaki da ayyukan ta'addanci da yunkurin kawowa kasar Sin baraka. Hukumomin jihar Xinjiang suna himmatuwa wajen yaki da ayyukan ta'addanci, da kafa cibiyar koyar da sana'o'i, matakan da ba kawai suka dace da dokokin kasar Sin ba, hatta ma sun bada babbar gudummawa ga ayyukan yakar ta'addanci a duniya baki daya. Kuma shaidu sun nuna cewa, matakan yaki da ayyukan ta'addanci da kawar da masu tsattsauran ra'ayi sun samar da tabbacin gaske ga zaman rayuwar al'ummar jihar ta Xinjiang, kamar yadda wata gogaggiyar 'yar jaridar kasar Masar ta ce, gwamnatin kasar Sin ta yi kokari wajen raya jihar Xinjiang, da kawo manyan sauye-sauye a jihar, kuma wasu rahotannin da kafafen yada labaran kasashen yamma suka ruwaito, sun jirkita gaskiya.

Ta'addanci makiyi ne na daukacin al'ummar duniya, a halin yanzu kuma duniya na cikin wani mawuyacin hali na yakar annobar COVID-19. Ko a fannin yaki da ta'addanci, ko kuma a fannin yaki da annobar, ya kamata Sin da Amurka su zama tsintsiya madaurinki daya. Amma akasin haka, akwai wasu 'yan siyasar Amurka wadanda suke yunkurin mara baya ga 'yan ta'adda, da lalata hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin yaki da annobar COVID-19 da bunkasuwa a duk duniya. Kamar yadda malam bahaushe kan ce, munafuncin dodo ya kan ci mai shi!(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China