2020-06-17 11:58:54 cri |
Shugabar hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD, Vera Songwe, ta ce kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, su ne muhimman abubuwan da za su farfado da nahiyar daga tasirin COVID-19.
Vera Songwe, ta bayyana yayin taron yini 5 ta kafar bidiyo, kan COVID-19 da kirkire-kirkire da zuba jari a Afrika cewa, kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire za su zama jigon farfadowar nahiyar daga annobar da kuma karfin nahiyar na samar da guraben ayyukan yi masu dorewa.
Shugabar hukumar ta jaddada cewa, nahiyar na bukatar kirkire-kirkire domin lalubo mafita na cikin gida, daga tasirin annobar COVID-19 da kuma matsalar tattalin arziki da ta jefa duniya.
Alkaluma na baya-bayan nan da cibiyar yaki da kandagarkin cututtuka ta Afrika ta fitar, sun nuna cewa, zuwa jiya Talata da rana, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin nahiyar ya zarce 251,866. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China