Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda ta bayyana jadawalin babban zaben kasar na 2021
2020-06-17 11:03:20        cri

Hukumar shirya zaben kasar Uganda ta sanar da jadawalin babban zaben kasar na shekarar 2021, inda ta jaddada aniyar daukar matakan kandagarkin annobar COVID-19.

Simon Byabakama, shugaban hukumar zaben kasar ya fadawa manema labarai cewa, za'a gudanar da zaben shugaban kasar da na majalisar wakilai da sauran zabukan kananan hukumomin kasar ne tsakanin 10 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.

Za a gabatar da sunayen masu shiga zabukan ne tsakanin watan Satumba zuwa Nuwambar shekarar 2020, kana za a gudanar da zaben fidda gwani tsakanin watan Nuwambar bana zuwa watan Janairun shekarar 2021.

Byabakama ya ce, ba za'a laminci yin gangamin yakin neman zabe ba saboda matakan da ake dauka na bayar da tazara da nufin dakile bazuwar cutar COVID-19.

Ya kara da cewa, hukumar za ta fitar da takardun neman sha'awar tsayawa takara a shafin intanet, za a iya ziyarta domin buga takardun daga shafin intanet.

Hukumar ta shawarci jam'iyyun siyasa da 'yan takara da su tabbatar an gudanar da zabukan fidda gwani da sauran shirye shirye cikin lumana. Kana an umarci 'yan takara, da wakilan jam'iyyu, da magoya baya, da su kiyaye dokokin game da taruwar jama'a kamar yadda ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China