Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafa dokar kiyaye tsaron kasa dama ce ta kyautata halin da yankin Hong Kong ke ciki
2020-06-16 21:29:36        cri
Kwanan baya ne, a birnin Shenzhen na kasar Sin, aka shirya taron sanin makamar aiki na kasa da kasa game da nacewa da kyautata tsarin "kasa daya tsarin mulki iri biyu" don tunawa da cika shekaru 30 da kaddamar da muhimmiyar dokar yankin Hong Kong. Masana da kwararru kusan 200 da suka fito daga babban yankin kasar Sin, da yankunan musamman na Hong Kong da Macau, da kasashen Rasha, Burtaniya, Jamus, Spania, India sun halarci taron. Mahalarta taron suna ganin cewa, matakin kafa dokar kiyaye tsaron kasa ta Hong Kong wata dama ce mai kyau wajen kawo karshen tashin hankali a yankin, zai kuma ba da tabbaci ga aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu" yadda ya kamata a yankin.

Saboda imanin da ake da shi kan yankin Hong Kong, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta baiwa yankin ikon kafa dokar kiyaye tsaron kasa a wasu fannoni bisa aya ta 23 dake cikin muhimmiyar dokar Hong Kong. Amma, bayan shekaru 23 da maido da Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, hakan bai tabbata ba, har ma wasu 'yan siyasa a ciki da wajen kasar, suna ta bata suna da 'yancin yankin, har ma wasu munanan ayyuka da aka gudanar ba bisa doka ba sun kawo barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna yankin, da illata yanayin kasuwancin yankin, da murkushe tsarin mulkin yankin, da kuma kawo kalubale kai tsaye kan tsaron kasar Sin baki daya.

Dokar kiyaye tsaron kasa tamkar kofa ce ta gida, ba zai yiwu ba a yarda barayi su shiga da ma fita daga gidan da babu kofa ba. Kiyaye tsaron kasa alhaki ne da aka dauka karkashin manufar "kasa daya tsarin mulki iri biyu", kuma ikon mulki ne na kwamitin tsakiya.

Shehun malami a sashen ilmin dokoki na jami'ar koyon kimiyya da fasaha ta Beijing Anthony Carty dan kasar Burtaniya, ya nuna a yayin taron cewa, dalilin da ya sa majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta inganta kafa dokar kiyaye tsaron kasa da ta shafi yankin Hong Kong, shi ne tashin hankali irin na karfin tuwo da aka samu, a yayin da ake kokarin kafa wasu tanade-tanaden tusa keyar masu aikata laifi wadanda suka gudu, lamarin da ya wuce karfin 'yan sandan yankin. Hakan na nuna cewa, kudurin da kasar Sin ta tsaida na kafa dokar kiyaye tsaron kasa ta Hong Kong, zabi ne da ya wajaba bisa hakikanin yanayin siyasa da ake ciki.

Akwai kuma wasu mahalarta taron da sun nuna cewa, bisa yanayin da ake ciki na kawo cikas ga tsaron kasa, matakin kafa dokar kiyaye tsaron kasa da ta shafi Hong Kong zai bunkasa da kyautata manufar "kasa daya amma tsarin mulki iri biyu", ko shakka babu matakin zai samarwa yankin sabuwar makoma mai kyau a nan gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China