Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tabbatar da zaman lafiya a duniya, shi ne kashin bayan kyautata rayuwar yara da samar musu kyakkyawar makoma
2020-06-16 18:25:40        cri

Rahoton shekara-shekara na Sakatare Janar na MDD kan yara da rikice-rikice da aka fitar jiya, wato rahoton dake nazarin tasirin da rikice-rikice kan yi kan rayuwar yara, ya ce a shekarar da ta gabata ta 2019, an keta hakkokin yara sama da 25,000 a wurare daban daban da ake rikici a fadin duniya.

A cewar rahoton, jimilar adadin ya yi daidai da wanda aka samu a shekarar 2018, wanda kuma ke nuna cewa, ana keta hakkokin yara 70 a kowacce rana.

Yayin da ake fama da rikice-rikice da rashin tsaro a fadin duniya, yaran da ba su ji ba, ba su gani ba, sun kasance gaba-gaba cikin wadanda ke fuskantar wahalhalu sakamakon rikice-rikicen.

Yara sun kasance masu rauni a duk inda suke, wanda ke nufin ba za su iya wani yunkurin kare kawunansu daga hadari ba. Akasari ma, yaran ba sa iya bambance abun da ke zaman hadari ga rayuwarsu da akasinsa.

A don haka, yaran dake rayuwa a kasashen dake fama da rikicin na fuskantar hadarin hare-hare kai tsaye, inda ake kashe su ko cin zarafinsu ko yi musu fyade ko horar da su matsayin mayaka ko sace su don neman kudin fansa ko ma amfani da su a matsayin garkuwa da dai sauran wasu munanan abubuwa dake illa ga rayuwa da lafiya da tunaninsu.

Hakika bangarorin dake rikici da juna da al'ummomi da uwa uba gwamnati, na da jan aiki a gabansu, wajen ganin sun kare yara tare da samar musu kyakkyawar makoma. Hakkin wadanan masu ruwa da tsakin ne tabbatar da aminci da lafiya da tsaron yara a ko da yaushe, a duk inda suke. Ya kamata bangarori masu adawa da juna su fahimci cewa, kare yara abu ne mai muhimmancin gaske idan har suna son a samu duniya mai kyakkyawar makoma a nan gaba. Saboda irin wadannan ayyuka na mummunan tasiri kan rayuwarsu.

Tabbas masu ruwa da tsaki sun gaza wajen kare yara, inda ake ci gaba da raba su da iyayensu da tilasta musu barin gida da lalata makarantunsu da asibitoci da sauran abubuwan dake kyautata rayuwarsu.

Kamata ya yi kare yara ya zama jigo cikin manufofin gwamnatoci da masu ruwa da tsaki. Kamata ya yi a kara ba da muhimmanci ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya da bude wuta, domin kare yara na tafiye ne kafada da kafada da warware tushen matsalolin dake haifar da rikice-rikice.

Akwai bukatar girmama dokoki da ka'idojin kasa da kasa. Wato ya kamata dukkan gwamnatoci ko kasashe da masu ruwa da tsaki, su mutunta dokokin kasa da kasa da suka tanadi kare yara da dukkan abubuwan da suka jibance su, kamar makarantu da asibitoci da sauransu. Ya kuma dace a kaucewa kai hare-hare wuraren dake zaman mazauni ko unguwannin jama'a.

Har ila yau, ya zama wajibi a tabbatar da tsaurara bibbiya da kai rahoton duk wani abu da ka iya yin barazana ga fararen hula da yara, tare da samar da tsuruka da dokoki masu karfi na hukunta wadanda ke keta hakkokin yara, domin ya kasance izina ga sauran jama'a.

Bugu da kari, sake gina rayuwar yara da aka ci wa zarafi na da matukar muhimmanci. Ware kudade domin sake farfado da rayuwar yara da rikice-rikice suka lalata, abu ne da ya zama wajibi. Akwai bukatar samar da shirye-shiryen da za su sauya musu tunani da horar da su da kuma tabbatar da lafiyarsu.

Ya kamata kasa da kasa su gaggauta daukan mataki tun kan wankin hula ya kai su dare. Kamata ya yi su yi dukkan mai yuwuwa wajen kawo karshen tasirin rikice-rikice a kan yara da kare su tun kan matsalar ta fi karfinsu.

Baya ga haka, samar da dabaru mabanbanta na kare aukuwar rikice-rikice da warwarsu ya zama tilas. Sannan kamata ya yi idan ana lalubo wadannan hanyoyi, a tabbatar da cewa yara sun zama jigo a cikinsu.

A cewar sakatare janar na MDD, zaman lafiya ita ce hanya mafi dacewa ta kare yara daga tasirin rikice-rikice.

Hausawa kan ce "da na kowa ne", duba da haka, hakkin kare su, nauyi ne da ya rataya ba kadai a kan gwamnatoci da masu adawa da juna ba, nauyi ne na bai daya da ya rataya a wuyan dukkan wadanda suka mallaki hankali. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China