Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ta sa aka samu sanin mene ne "hakkin dan adam" a idon kasar Amurka
2020-06-14 20:07:22        cri

Kasar Amurka ta dade tana bayyana kanta a matsayin wata kasa dake "kare hakkin dan Adam" a duniya, sai dai annobar COVID-19 ta ba mu damar sanin ainihin ra'ayin kasar game da hakkin.

Wani abin da ya fi muhimmanci cikin hakkin dan Adam shi ne hakkin rayuwa da samun tsaron lafiya. Amma ta yaya kasar Amurka take kare rayukan jama'arta daga cutar COVID-19? Maimakon daukar matakan kandagarkin cutar, da baiwa jama'a kayayyakin da suke bukata domin kare kansu, ta zabi kare moriyar manyan 'yan kasuwa da masu masana'antu. Ban da wannan kuma, ta mai da aikin dakile cutar wani batu ne na siyasa, inda 'yan siyasan kasar ke kokarin cacar baki da juna, tare da kawo cikas ga aikin lafiyar kasar. Wani nazarin da jami'ar Columbia ta kasar Amurka ta gudanar ya nuna cewa, da a ce an dauki matakin zaman gida mako guda kafin ainihin lokacin da aka fara gudanar da matakin, to, da mutane a kalla dubu 36 ba za su mutu ba. A ko ina ana kokarin dakile cutar ta hanyar sanya dokar zaman gida da takaita zirga-zirga, amma gwamnatin kasar Amurka ta kasa yin haka, kafin ta ji yadda jama'arta suke kuka da ihu da babbar murya.

Ban da wannan kuma, hakkin dan Adam ya shafi yadda wani mutum ke iya samun mutunci da daidaituwa a cikin wata al'umma. Sai dai a kasar Amurka, cutar COVID-19 ta nuna yadda ake nuna rashin daidaito a tsakanin al'ummomin kasar. Inda masu kudi da mukami ke samun damar gwajin kwayoyin cutar cikin sauki, yayin da talakawa ke shan dimbin wahalhalu kafin su iya samun damar yin gwajin. Kana kabilanci ya sanya 'yan asalin Afirka da na Latin Amurka dake kasar Amurka jin radadi sosai. Misali, a jihar Michigan, yawan 'yan asalin Afirka ya kai kashi 12% na yawan al'umma, amma su bakaken fata sun kai kashi 33% cikin wadanda suka kamu da cutar COVID-19, kana sune kashi 40% na wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar. Ina adalci? Kuma ina hakkin dan Adam cikin wannan al'amari?

Hakkin dan Adam ya shafi yadda ake kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe, don tabbatar da cikakken hakki na daukacin bil Adama na duk duniya. Sai dai menene matakan da kasar Amurka ta dauka a duniya? Tana kokarin shafawa kasar Sin kashin kaza, da dora laifi ga hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da dakatar da hulda da ita, gami da kakabawa kasashen Iran, da Cuba, da Venezuela takunkumi, da yin barazana ga kasar India, da sauran kasashe, a yunkurin kwatan kayayyakin kandagarkin cuta da take bukata.

Ta wadannan misalai za mu iya fahimtar mene ne ma'anar "hakkin dan Adam" a idon kasar Amurka. Hakika a ganinta, kalmar nan ba wani abu ba ne, illa dai wani abin da wasu 'yan siyasa da attajiran kasar ke yin amfani da shi wajen tabbatar da moriyarsu, gami da yin babakere a duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China