Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'anar "Mayar da moriyar jama'a a gaban kome" ta Xi Jinping
2020-06-14 17:19:12        cri
"Dole ne a tsaya kan mayar da moriyar jama'a a gaban kome, da dogaro da jama'a, da kara samar da alheri ga jama'a, da shiga ayyukan jama'a, kana da tabbatar da hakan a yayin da ake tsara manufofi da gudanar da ayyuka daban daban, ciki har da ayyukan dakile annobar COVID-19 da nemo ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasar." Wannan ne jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin manyan taruka biyu wato taron CPPCC da na NPC na bana, inda ra'ayin "Mayar da moriyar jama'a a gaban kome" ya samu karbuwa a yanar gizo.

A rangadin aikin da Xi Jinping ya yi a wurare daban daban na kasar, sau da yawa ya bada umurni ne bisa wannan ra'ayin neman ci gaba.

A tsakanin ranar 8 zuwa 10 ga watan Yuni, Xi Jinping ya yi rangadi a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai. A ranar 9 ga wata, ya ziyarci lambun kare halittu na yawon bude ido a kusa da tsaunin Helan, na birnin Yinchuan dake jihar, inda ya yi hira da mazauna wurin, ya kuma jaddada cewa, a yayin da ake kokarin bunkasa aikin gona na zamani da sana'ar yawon shakatawa ta al'adu, tilas ne a mayar da moriyar jama'a a gaban kome, wato dora muhimmanci kan matsayin manoma, da maida moriyar manoma a gaban komai.

A tsakanin ranakun 11 da 12 ga watan Mayu, Xi Jinping ya yi rangadi a lardin Shanxi, inda ya maida aikin kawar da talauci a matsayin wani muhimmin batu. Ya ce, wa'adin cimma burin kawar da talauci na kusantowa. A yayin da ya ziyarci a sabon kauye na Fangcheng, Xi Jinping ya gayawa mazauna wurin cewa, jam'iyyar JKS na kokarin neman moriya ga jama'a, yanzu ba a karbi haraji da hatsi da kudi a wasu fannoni daga wajen manoma ba, a maimakon haka, an baiwa masu fama da talauci magunguna, da gidaje, da koya musu fasahohi, da taimaka musu neman hanyar samun wadata, Xi Jinping ya yi imanin cewa, manoma zasu kara samun kyautatuwar zaman rayuwa a nan gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China