Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Ba za a bar wata kabila a baya ba
2020-06-12 16:30:54        cri

Daga ranar 8 zuwa 10 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadi zuwa sassa daban daban na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai zaman kanta da ke arewa maso yammacin kasar. A yayin rangadinsa zuwa unguwar Jinhuayuan da ke birnin Wuzhong na jihar, ya ce, "Dukkan kabilu al'ummar kasar Sin ne, kuma ba za a bar kowace kabila a baya ba, a kokarin da ake na saukaka fatara da gina al'umma mai matsakaiciyar wadata, da kuma zamanitar da harkokin rayuwa." Kalaman da ya karfafa gwiwar mazauna yankin.

Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, daya ne daga cikin jihohin kasar Sin 5 masu cin gashin kansu, inda kuma ke da kabilu da dama kamar Han, da Hui, da Uygur da dai sauransu. Unguwar Jinhuayuan na birnin Wuzhong da shugaba Xi ya ziyarta, na da mazauna na dindindin 13,850, ciki har da 'yan kabilun Han da Hui da Man da Mongoliya da Zang da sauransu, wadanda suke zauna lafiya da juna. Bisa jerin manufofin shugabanci da kirkire-kirkire, yankin ya zama wani abun misali na hadin kai da ci gaban kabilun kasar Sin.

Kasar Sin kasa ce da ke da kabilu 56. Bana ta kuma kasance shekarar da kasar za ta fitar da dukkanin al'ummar kasar da ke fama da talauci daga kangin da suke ciki. Sai dai a sakamakon yadda dimbin al'ummar 'yan kananan kabilu suke rayuwa a sassa da ke matukar fama da talauci, shi ya sa kawar da talauci daga yankunan 'yan kananan kabilu ya zama wani muhimmin aikin da ake sanyawa gaba wajen saukaka fatara.

A hakika, a 'yan shekarun baya, sau da dama ne shugaba Xi Jinping ya kai rangadi sassan da 'yan kananan kabilu ke zama, inda ya tattauna tare da su don gano bakin zaren warware matsalar talauci.

Bisa kokarin da ya yi, sassan 'yan kananan kabilu sun samu gagarumar nasara wajen saukaka fatara. Ya zuwa watan Nuwamban bara, daga cikin kananan kabilu 28 da ba su da yawan mutane a kasar, akwai kabilu 25 da aka fitar da gaba dayansu daga kangin talauci. Al'ummar kananan kabilu suna ta kara jin dadin rayuwarsu bisa manufofin da ake aiwatarwa na tallafa musu.

A ranar 20 ga watan Mayun da ya gabata, da ya ji labarin dukkanin 'yan kabilar Maonan sun fita daga kangin talauci, shugaba Xi Jinping ya ce, na yi farin ciki matuka da jin hakan. Ba za mu bar wata kabila a baya ba, a kokarin da muke yi na gina al'umma mai matsakaiciyar wadata. A 'yan shekarun baya, bi da bi ne 'yan kananan kabilu da dama sun fito daga kangin talauci, abin da ya zama muhimmiyar nasara da muke samu wajen saukaka fatara. Da fatan kuma daga wannan sabon mafari za mu ci gaba da kokartawa, ta yadda za a kara jin dadin rayuwa."

Sinawa na daukar ruman, a matsayin abun da ke alamanta alheri, kuma shugaba Xi Jinping ya taba bayyana kabilun kasar 56 a matsayin 'ya'yan ruman, don bayyana yadda suke rungumar juna. A kokarin da ake yi na fitar da dukkanin al'ummar kasar Sin daga kangin talauci, ba za a bar wata kabila a baya ba. Wannan al'adar al'ummar Sinawa ce, haka kuma abu ne da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin ya bukata. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China