Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo Na Tafiyar Da Harkokin Jakadanci A Matsayin Makaryaci
2020-06-10 21:14:09        cri
Kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo wanda ya yi alfahari da yin karya, ya sake shafa wa kasar Sin kashin kaji, inda ya ce, kasar Sin ta baza labarum karya dangane da mutuwar Ba'amurke dan asalin Afirka George Floyd. Kalaman Pompeo sun wuce zaton mutane, ya hada kasar Sin da mutuwar wannan Ba'amurke dan asalin Afirka. Kila marubuci mafi kwarewa a duniya bai iya rubuta kagaggen littafi irin wannan ba.

Har kullum kasar Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, balle ma kasar Amurka. Mike Pompeo ya yi amfani da mutuwar George Floyd ne abin tausayi, ba kasar Sin ba ce.

Shaidu sun tabbatar da cewa, baza labarai marasa gaskiya, yin magudi da yi wa duniya sharri, su ne hayayyar da Mike Pompeo da sauran 'yan siyasa irinsa, inda suke yin karya wajen tafiyar da harkokin diplomasiyya.

Kwanan baya, jaridar The New York Times ta rubuta wani sharhi, inda ta yi nazari kan dalilin da ya sa shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta ce ba za ta halarci taron koli na G7 da za a shirya a karshen watan Yunin bana ba. Sharhin ya ruwaito manyan jami'an Jamus na cewa, daya daga cikin muhimman dalilan shi ne Jamus ba ta goyi bayan nuna kiyayya ga kasar Sin ba.

Hakika kasashen duniya sun san yunkurin Mike Pompeo da sauran 'yan siyasa kamar shi. Ba za a iya yi musu magudi ba.

A halin yanzu duk wani dan siyasar dake da mutunci, ba zai yarda ya hada kansa ko ya yi mu'amala da marasa gaskiya kamar Pompeo ba. Tabbas Amurka za ta ji kunya kan yadda Mike Pompeo yake shirga karya, wajen tafiyar da harkokin diplomasiyya kasar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China