Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban taron kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam na kasa da kasa na shekarar 2020 zai gabatar da bikin baje koli ta yanar gizo
2020-06-10 14:39:16        cri
An gudanar da wani taron share fage a jiya Talata, kwanaki 30 gabanin babban taro kan fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam(AI) na kasa da kasa na shekarar 2020 a birnin Shanghai na kasar Sin.

Gwamnatin birnin Shanghai ce za ta jagoranci gudanar da babban taron, wanda za a yi daga ranar 9 zuwa ranar 11 ga watan Yuli. Taken taron na bana shi ne "hada kasa da kasa tare ta fasahar AI", wanda kuma shi karo na farko da za a gudanar da bikin baje kolin ta yanar gizo, inda kimanin kamfanoni 150 za su halarta.

Tun daga shekarar 2018, ya zuwa yanzu, an cimma nasarar gudanar da babban taron fasahar kwaikwayon yanayin tunanin dan Adam na kasa da kasa sau biyu, har taron ya ba da muhimmin tasiri ga kasa da kasa, bisa bunkasuwar fasahohin AI a birnin Shanghai na kasar Sin.

Haka zalika kuma, bisa jagorancin babban dakin watsa shirye-shirye na birnin Shanghai, za a gudanar da shirye-shiryen taron, kamar bikin budewa, da cikakken zaman taro da sauransu, cikin hadin gwiwa da dakunan watsa shirye-shirye dake kasashen Amurka, Jamus, Faransa da kuma Singapore da dai sauran wurare.

A halin yanzu, an riga an gayyaci wasu kwararru a wannan fanni, da shugabannin manyan kamfanonin da abin ya shafa dake kasar Sin da kasashen ketare, da wasu wakilan kungiyoyin kasa da kasa, kimanin mutane 500 don su halarci taron. Kuma 80% daga cikinsu, sun riga sun amince da halartar taron, ciki har da wasu masu lambobin yabo na Turing da Nobel, da shugabannin manyan kamfanoni a wannan fanni, wadanda suka hada da IBM, da SAP, da kuma Amazon da sauransu.(Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China