Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta samar da tsari na musamman na rarraba kudaden gudanarwa
2020-06-10 11:49:39        cri
Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin samar da wani sabon tsarin rarraba kudaden gudanarwa, ta yadda mutane, da sana'o'i za su rika amfana kai tsaye, daga rangwamen da gwamnatin ke samarwa.

Yayin taron majalissar gudanarwar kasar na jiya Talata, wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta ne aka amince da samar da tsarin, wanda zai baiwa kananan yankuna, da gundumomi damar samun kudaden ayyuka kai tsaye, kuma a kan lokaci.

Karkashin tsarin, kasar Sin za ta fadada musaya, da biyan kudade tsakanin gwamnatin tsakiya da kananan hukumomi, tare da tsara hanyoyin biyan kudi daga nau'o'in asusun da gwamnati ke lura da su. A daya hannun kuma, a bana, mahukuntan na Sin sun amince da zaftarewa kamfanoni kudaden haraji, da sauran wadanda ake biya da kimanin yuan tiriliyan 2.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 354.

Da yake wannan mataki na iya sanya kananan hukumomin kasar cikin matsi na kudade, gwamnati ta amince da samar musu yuan tiriliyan 2, ta yadda za a tabbatar da aiwatar da matakan agaji a matakai na kasa.

Kaza lika yayin da ake tsara yanayin amfani da kudade, an bukaci kananan hukumomi da su mayar da hankali ga rage fatara, ta yadda za a kai ga cimma kudurorin da aka tsara a fannin cikin wannan shekara.

Taron ya kuma amince da fitar da karin matakan saukakawa kamfanonin waje, damammakin gudanar da harkokin su, sashen da aka yi amanar na samar da guraben ayyuka har kusan miliyan 200.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China