Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwastam: Jimillar kudaden cinikayyar waje na Sin a watanni 5 na farkon bana sun kai yuan tiriliyan 11.54
2020-06-08 14:02:18        cri

Hukumar kwastam ta kasar Sin, ta ce jimillar kudaden cinikayyar waje na kasar Sin a watanni 5 na farkon shekarar bana, sun kai yuan tiriliyan 11.54, adadin da ya yi kasa da kaso 4.9 bisa dari, idan an kwatanta da makamancin lokaci a bara.

Alkaluman kididdiga na hukumar sun nuna cewa, adadin kudaden hajojin da aka fitar a wannan tsakani sun kai yuan tiriliyan 6.2, wanda ya yi kasa da kaso 4.7 bisa dari, yayin da na hajojin da aka shigo da su cikin kasar ya kai yuan tiriliyan 5.34, wanda shi ma ya yi kasa da kaso 5.2 bisa dari.

Babban darakta a sashen binciken alkaluman kididdiga na hukumar Li Kuiwen, ya ce alkaluman hukumar, na iya karuwa a fannin hajojin da kasar ta fitar a watan da ya gabata.

Li Kuiwen, ya kara da cewa, duk da zurfafar komadar tattalin arzikin duniya, matsin da bangaren cinikayyar waje na Sin ka iya fuskanta ba shi da yawa, hakan kuwa ya biyo bayan nasarar matakan kandagarki da shawo kan cutar da aka cimma. A hannu guda kuma, kamfanoni masu sarrafa hajoji a kasar Sin, sun yi cikakken amfani da damar su ta komawa bakin aiki yadda ya kamata, sun samar da kayayyakin da duniya ke bukata, sun kuma ingiza bukatar fitar da hajoji zuwa ketare. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China