Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19: Sashen yawon bude ido na Afirka na fuskantar kalubale
2020-06-08 11:15:12        cri

 

A farkon wannan shekara, hukumomin yawon shakatawa na kasa da kasa, sun yi hasashen samun ci gaba a harkar yawon bude ido a sassan nahiyar Afirka, suna masu fatan baki daga kasashe daban daban, za su kara yawaita ziyartar irin wadannan wurare dake nahiyar, da karuwar da ta kai kaso 3 zuwa 5 bisa dari a shekara guda.

To sai dai kuma, bullar cutar COVID-19, ta tilasawa kasashen Afirka da dama, aiwatar da matakai masu tsauri na kandagarkin cutar, kuma har ya zuwa yanzu, da yawa daga jiragen saman kasa da kasa ba sa gudanar da sufurin fasinjoji, yayin da kuma kasashe da yawa ke aiwatar da dokar kulle, aka kuma rufe birane da dama, lamarin da ya sa harkar yawon bude ido tsayawa cak.

Kididdiga ta nuna cewa, yawan mutanen dake aiki a fannin yawon bude ido a kasashen Kenya, da Afirka ta kudu, da Tanzania da sauran wasu kasashen nahiyar, ya kai mutum miliyan daya. Sai dai kuma sakamakon bullar wannan annoba, otel otel, da wuraren cin abinci, da na yawon bude ido sun fuskanci babbar hasara.

 

 

Har yanzu dai ba a san ko yaushe ne kasashen Afirka za su kai ga sake bude kofofin su, a kuma kai ga sake komawa hada hadar yawon bude ido.

A wani bangaren kuma, a halin da ake ciki, filayen jiragen saman nahiyar na gudanar da jigilar fisinjojin dake komawa gida, da dakon kayayyaki ne kadai, yayin da mafi yawan masu jigilar fasinjoji suka dakatar da ayyukan su.

A cewar kungiyar yawon shakatawa ta duniya, akwai alamu dake nuna cewa, za a iya kaiwa ga watanni 10 masu zuwa ko fiye, kafin fannin yawon shakatawa na Afirka ya sake farfadowa daga tasirin barkewar wannan annoba.

Masana a fannin na ganin tun da dai sashen ba zai iya samun farfadowa cikin sauri ba, ko shakka ba bu yana bukatar tallafin gwamnati, da ma sauran sassa masu nasaba da shi, kamar na amfani da na'urorin zamani a fannin sufuri, da neman masaukai, wadanda za su karfafa gwiwar masu yawon shakatawa, har ya kai ga farfadowar sashen yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China