Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai Da Jama'a A Gaban Kome Manufa Ce Mafi Muhimmanci Da Kasar Sin Ta Dauka Wajen Yakar Cutar COVID-19
2020-06-07 20:14:50        cri

A yau Lahadi, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da takardar bayani dangane da matakan da kasar ta dauka a kokarin dakile cutar COVID-19, don raba fasahohin da kasar ta samu a fannonin hana yaduwar annobar, gami da jinyar wadanda suka kamu da ita, da neman karfafawa kasashen duniya gwiwa a kokarinsu na hadin gwiwa da juna don ganin bayan mummunar cutar.

Idan an yi nazari kan wannan takardar bayani, za a ga cewa wata babbar manufar da aka nuna, ita ce mayar da jama'a da moriyarsu a gaban kome, gami da ceto rayukan jama'a ba tare da tsimin kudi ko albarkatu ba. Hakika wannan manufa ita ce fasaha mafi muhimmanci da kasar Sin ta samu, bisa kokarinta na neman shawo kan cutar, wanda ya samu nasara bayan da aka shafe watanni 3 ana gudanar da aikin.

Manufar mayar da jama'a a gaban kome na nufin, a dinga mayar da cikakken hankali kan moriyar jama'a, da dogaro kan jama'ar kasar da hadin gwiwa tare da su a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19.

A nasa bangaren, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata bukatar kallon rayuka da lafiyar jikin jama'a a matsayin abu mafi muhimmanci. Bisa wannan umarnin da ya yi ne, an yi ta kokarin neman kwararrun likitoci, da na'urori masu inganci, da sauran albarkatun da ake bukata, don kyautata aikin jinyar wadanda suka harbu da cutar. Zuwa ranar 31 ga watan Mayun da ya gabata, yawan mutanen da suka warke bayan kamuwa da cutar a kasar Sin ya kai kashi 94.3%.

A fannin farfado da tattalin arziki ma haka lamarin yake, wato ana dogaro kan jama'a domin kowa ya samar da gudunmawa a kokarin maido da kasuwanci da masana'antu a kasar, don tabbatar da moriyar dukkan al'ummun kasar.

Ganin haka ya sa Sinawa samun cikakken karfin gwiwa, na samun cimma burikan da suka sanya a fannin raya kasarsu, da tabbatar da wata makoma mai haske a kasar, gami da samar da gudunmawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China