Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayanin ayyukan yaki da cutar COVID-19 ta Sin ta shaida kokarin kasar wajen inganta tsarin kiwon lafiyar dan Adam
2020-06-07 16:06:02        cri
A yau ne, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayanin ayyukan yaki da cutar COVID-19 ta kasar Sin, inda aka yi bayani game da matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar COVID-19, wadanda aka kasa su zuwa kaso hudu, wato kokarin Sin wajen yaki da cutar COVID-19, da ayyukan hadin gwiwa na magance cutar da bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar, da yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar da sauran kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa, da kuma kokarin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama a fannin kiwon lafiya.

A halin yanzu, dukkan 'yan Adam na fuskantar kalubalen kiwon lafiya na duniya mafi tsanani tun bayan yakin duniya na biyu. Kasar Sin ta yi namijin kokarin yaki da cutar, da tabbatar da tsaron rayuka da lafiyar jama'ar kasar. Sin ta dauki matakai a dukkan fannoni wajen magance cutar, da kula da jinyar dukkan mutanen kasar da suka kamu da cutar, don haka an samu nasarori wajen yaki da cutar.

Takardar ta yi nuni da cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa babban makami ne wajen yaki da cutar. Sin ta dauki alhakin dake bisa wuyanta, da gabatar da sakwanni a fili, da kuma mika dukkan abubuwan dake shafar cutar ga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da kuma kasashen da abin ya shafa, tare da samar da gudummawa da amfani da fasahohi wajen yaki da cutar ga duk duniya baki daya.

Ya zuwa karshen watan Mayu, Sin ta riga ta samar da gudummawa ga kasashen kimanin 150 da hukumomin kasa da kasa 4, da tura tawagogin masanan kiwon lafiya ga kasashe 24 da suka fi bukata, da gudanar da tarukan magance cutar ta yanar gizo ga kasashen duniya fiye da 170, da kuma kara samar da kayayyakin likitanci da na'urori ga duk duniya baki daya. Mutane daga bangarori daban daban na kasa da kasa sun yi nuni da cewa, Sin ta bi tunanin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da daukar alhakinta, kasa da kasa sun nuna yabo gare ta a wannan fanni.

Yan Adam suna iya warware manyan matsalolin cutuka ta hanyar yin hadin gwiwa da yin kokari tare. Yayin da ake tinkarar cutar COVID-19, jama'ar kasa da kasa sun yi kokari tare da yin hadin gwiwa don yaki da cutar tare. A halin yanzu, yaduwar cutar COVID-19 ba ta kare ba, ana bukatar kasa da kasa su ci gaba da yin kokari da daukar matakai don magance cutar. Ya kamata hukumar WHO ta ci gaba da bada jagoranci wajen gudanar da ayyukan magance cutar, da kara nuna goyon baya ga kasashen Afirka, da kyautata tsarin kiwon lafiya na duniya, da kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don inganta karfin duk duniya wajen yaki da cutar.

Takardar bayani game da matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar COVID-19 ta shaida kokarin kasar wajen inganta tsarin kiwon lafiyar dan Adam, wanda za a iya tabbatar da tsaron rayuwa da lafiyar dukkan dan Adam. Lafiyar dan Adam tushe ne na samun ci gaban zamantakewar al'ummar kasa da kasa. Idan ana son samun kyakkyawar makomar dan Adam, to ya kamata a yi kokarin tabbatar da lafiyar dan Adam, da kuma kokarin ba da muhimmanci matuka ga lafiyar jama'a. Kuma a yayin da dukkan 'yan Adam ke fuskantar matsalar kiwon lafiya, hadin gwiwa ce hanya mafi dacewa wajen yaki da cutar da tabbatar da lafiyar dukkan 'yan Adam baki daya. (Zainab Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China