Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa wasu shugabannin kasashen yanma ba su tsokaci kan masifun da wariyar launin fata ke haifarwa a Amurka?
2020-06-06 16:22:24        cri

Yanzu haka ana zanga-zanga a kai a kai a sassa daban daban na fadin Amurka, sakamakon rasuwar George Floyd, 'dan asalin Afirka dake kasar. Al'ummun kasa da kasa sun yi suka da kakkausar murya kan wariyar launin fata da ta dade tana kasancewa a kasar ta Amurka, amma wasu shugabannin kasashen yamma wadanda ke son jaddada demokuradiyya da hakkin dan Adam ba su ce uffan ba.

Misali yayin da aka yi wa firayin ministan kasar Canada, Justin Trudeau tambayoyin dangane da batun, sai ya bayyana cewa, zai mai da hankali ne kan aikin kula da al'ummun kasarsa kadai, kana bayan mako guda da aukuwar lamarin, takwaransa na Birtaniya Boris Johnson, shi ma ya bayyana cewa, babu wariyar launin fata a kasarsa kawai.

shugabannin kasashen yamma ba su yi tsokaci kan matakan ban mamaki da shugabannin Amurka suka dauka ba, lamarin da ya sabawa al'adarsu ta yin sharhi kamar yadda suke so kan al'amuran kasa da kasa.

Hakika wasu kasashen yamma sun saba da bin umurnin shugabannin kasar Amurka, musamman ma tun bayan da suka gano matakan da Amurka ta dauka a kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya da tsaron kasa.

Kana a cikin wasu kasashen yamma, kamar su Birtaniya da Australia da Canada da sauransu, akwai yiyuwar samun matsalar wariyar launin fata, don haka ana iya cewa, tsoro ne dalilin da ya sa suka yi shiru kan batun.

Amma abun mamaki shi ne, yadda wadannan 'yan siyasar kasashen yamma da ba sa iya warware matsalar wariyar launin fata a kasashensu, kan shafawa kasashe masu tasowa bakin fenti.

Hakika wariyar launin fata babbar matsala ce da ta dade a gaban mahukuntan kasar Amurka, ita ce kuma matsalar da kasashen yamma suke fuskantar tare, don haka, ya dace su warware matsalar tun da wuri. Kana wasu kasashen yamma sun riga sun sha wahala saboda sun koyi dabarun yaki da annobar cutar COVID-19 na Amurka, ko suna son ci gaba da shan wahala wajen matsalar wariyar launin fata kamar yadda Amurka take?(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China