Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kula da halittu harka ce ta dan Adam
2020-06-06 15:37:32        cri
Ranar 5 ga wata, ranar muhalli ce ta duniya, a wannan shekara ta bana, an mai da hankali kan muhallin halittu da kasancewar halittu iri daban daban. Taken ranar muhalli ta duniya na bana shi ne "Kula da halittu cikin gaggawa." Ana iya cewa, wannan gargadi ne da shirin kare muhalli na MDD ya yi ga daukacin 'yan Adam, wannan ne kuma alhakin da gwamnatin kasar Sin ta daukarwa kanta wajen raya wayin kan hallitu na kasar, wanda yake bukatar dukkan Sinawa su shigar da shi cikin rayuwarsu, kuma daga daidai wannan lokaci na yanzu, mu kula da halittu da kuma kare muhalli.

Yanayin hallitu da muke ciki a yanzu na samun babban sauyi. Bisa kididdigar da hukumar kula da yanayi ta duniya ta bayar, an nuna cewa, shekaru goma wato daga shekarar 2010 zuwa ta 2019, sun kasance shekarun da aka fi fama da yanayin zafi tun bayan da aka soma ajiye bayanai, a shekarar 2019, matsakaicin yawan zafin duk duniya ya kai digiri 1.1 Celsius, sama da matakin kafin masana'antar duniya. An samu irin canjawar ma a nan kasar Sin, tun daga shekarar 1951, matsakaicin yanayin zafi a kasar ya karu da digiri 0.24 Celsius a kowace shekara. Canjin yanayi ya hanzarta narkewar dusar kankara, da kara zafin kasa da na teku, da gaggauta saurin karuwar tsayin teburin teku, kuma ya kawo tasiri sosai ga lafiyar bil adama, cigaban tattalin arziki, samu isassun abinci, da kuma tsarin muhallin halittu na kasa da na teku.

Game da sauyin yanayi, wato kalubalen bai daya da duk duniya ke fuskanta, kasar Sin ta dauki alhakin dake bisa wuyanta a matsayin wata babbar kasa: samar da kudin RMB yuan biliyan 20 don kafa asusun hadin kan kasashe masu tasowa kan sauyin yanayi na kasar Sin, don taimakawa kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi; sanya hannu kan yarjejeniyar Paris; inganta hadin kai a fannin sauyin yanayi tsakanin bangarori masu dama da kuma mayar da raya "hanyar neman ci gaba ba tare da bata muhalli ba" matsayin wani muhimmin abu dake cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya".

Abu mafi muhimmanci shi ne, yanzu dai a nan kasar Sin ana ta kara amincewa ra'ayin "ruwa mai tsabta da koren dutse su ne zinari". Mai da kiyaye muhallin halitu da samun ci gaba ba tare da bata muhalli ba, sun kasance hanyar da wurare daban daban na kasar suke bi wajen neman bunkasuwa.

Kasar Sin na kara bayyana kyawawan yanayin da take ciki irin na kasancewar jituwa a tsakanin dan Adam da halittu.

'Yan Adam za su wahala idan muhallin halittu ya gurbace, don haka, kula da halittu yana nufin kula da yan Adam. Yanzu, duniyar da muke rayuwa na fama da annobar cuta ta COVID-19. Kwayar cutar ta kara tunatar da mu cewa, duniya kamar babban iyali ne, yan Adam na da makomar bai daya. Dole ne mu mai da hankali sosai kan alakar yan Adam da halittu, kuma mu mutunta halittu, da kiyaye halittu tare. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China