Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko akwai 'yancin bayyana ra'ayi a Amurka?
2020-06-03 20:28:36        cri

Kwanan baya wani mai jagorancin shiri a tashar CNN ya bayyana cewa, "Ban taba ganin irin wannan lamari ba!" saboda ya ga an tsare abokin aikinsa bakar fata 'dan asalin kasar Amurka, yayin da yake gabatar da rahoto a wurin zanga-zangar da aka yi, kana 'yan sandan Amurka sun taba harbin wata 'yar jarida ta kasar a idonta na hagu da harsashin roba, yayin da take aiki a kan titi.

Yanzu haka ana yin zanga-zanga a kai a kai a sassan kasar ta Amurka, don haka 'yan sanda su kan kai hari ga 'yan jarida wadanda suke gabatar da rahotanni, amma har kullum Amurka tana mayar da kanta a matsayin babbar kasa mai 'yancin bayyana ra'ayi, amma yanzu ko 'yan jarida ba su da 'yancin gabatar da labarai na gaske, ana zaton 'yan siyasar Amurka ba su da hankali ke nan.

Kan wannan, Dan Shelley, mai jagorar kungiyar watsa labarai ta rediyo da talibiji ta Amurka ya bayyana cewa, matakin da 'yan siyasar kasar suka dauka, yana lahanta 'yan jarida, har yana lahanta al'ummun kasar baki daya, saboda hakan zai hana a kalli, ko daukar bidiyo kan al'amuran da suke faruwa. Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric shi ma ya jaddada cewa, da zarar an kai hari ga 'yan jarida, to duk zaman takewar al'ummun kasar za ta jigata.

Hakika tun bayan da gwamnatin Amurka ta wannan karo ta fara mulki a kasar, ta kan matsa lamba ga kafofin watsa labarai, wato shugabnanin kasar su kan mayar labaran dake shafar suka kan su, a matsayin labarai na jabu. Misali a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, shugaban kasar ya yi cacar baki ta dandalin sada zumunta na Twitter, a karshe dai ya sa hannu kan wani umurnin kayyaden aikin dandalin, lamarin da ya gamu da suka daga al'ummun kasa da kasa.

An lura cewa, tun bayan barkewar annobar COVID-19, sau da dama 'yan siyasar Amurka suna baza jita-jita, suna dora laifi ga wasu, har suna kai suka ga 'yan jarida. Kwanan baya, jaridar New York Times ta fitar da wani rahoto, inda a cikin sa aka bayyana cewa, 'yan leken asiri na Amurka sun taba yin koken cewa, akwai wahala matuka su gabatar da bayanai ga shugaban kasar, saboda ya kan nuna ra'ayi maras tushe, ba ya son amincewa da bayanan da suka sabawa tunaninsa.

Kawo yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar COCID-19 a Amurka, ya riga ya kai miliyan 1 da dubu 850, kana ana yin zanga-zanga a kai a kai a biranen kasar sama da 140, amma wadannan 'yan siyasa masu son kai, suna ci gaba da dora laifi ga saura, domin rufe hakikanin yanayin da kasar ke ciki.

Labarai na gaske hoto ne mafi ma'ana, saboda za su samar da hakikanin abubuwa ga al'ummun kasar, kuma ko shakka ba bu, yunkurin yaudara na 'yan siyasar Amurka zai ci tura.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China