Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kowa ne Tsuntsu kukan gidansu yake yi
2020-06-03 16:26:04        cri
A yayin zaman wakilan NPC da aka shirya a watan Mayun, an sanar da saka batun tsarawa da inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong gami da tsarin aiwatar da ita a cikin ajandar taron. Bayan sanar da muhimmiyar doka da kasar Sin ke fatan kafawa don kare muradun da 'yanci da martabar kasa da daukacin Sinawa, ta yadda zai dace da halin da ake ciki, sai katsam wasu 'yan siyasar kasashen yammacin duniya, ciki har da sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, sun bayyana cewa, wai wannan matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka zai kawo karshen tsarin cin gashin kai da ake aiwatarwa a Hong Kong, har ma Amurkar ta yi shelar kawo karshen matsayin musamman da ta yi wa yankin Hong Kong a kwanan baya. Shin Amurka ta manta da karin maganar malam Bahaushe, "Iya ruwa fidda kai?" Don haka, kowa ya kashe wutar gabansa.

Kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya, za a kuma yi hakan ne da kafa dokokin da za su dace da ita, abin da malam Bahaushe ke cewa, kowane Tsuntsu kukan gidansu yake yi, maimakon ara ka yafa.

Tun bayan da yankin Hong Kong ya dawo hannun babban yankin kasar Sin, bisa ka'ida ta 23 cikin babbar dokar Hong Kong, gwamnatin tsakiya ta kasar ta damkawa yankin izinin kafa dokarta ta fannin kiyaye tsaron kasa. Amma kawo yanzu, ba'a kammala aikin kafa dokar ba, al'amarin da ya sa yankin Hong Kong ya zama wani wurin dake fuskantar rashin doka a bangaren tsaron kasa.

Yanzu dai, taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC na 13 ya zartas da kundin kafa dokar tsaron yankin Hong Kong domin kokarin inganta tushen manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", ta yadda za'a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin na Hong Kong.

Sanin kowa ne cewa, idan gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kara inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin Hong Kong, hakika, masu hana ruwa guda, kamar 'yan siyasar Amurka da 'yan kanzaginsu, ba za su samu damar yin shisshigi a harkokin yankin ba, sannan yunkurinsu na kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da yankin na Hong Kong zai bi ruwa. Ai dama sai Bango ya tsage Kadangare ke samun wurin shiga.

Abin tambaya shi ne, rashin doka ne ya haifar da boren dake faruwa a sassan Amurka ko mene ne? Idan haka ne, abin da Amurkar ke fatan ganin yana faruwa ke nan a wasu kasashe? Idan bore shi ne adon 'yanci a bangaren Amurka, to hakika ba haka lamarin yake a sauran kasashe na duniya ba, burin kasashe masu 'yanci dake kishin muhimman muradun al'ummomin su, shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama'a maimakon zangar-zangar da za ta kai ga koman bayan kasa da al'ummarta a dukkan fannoni. Da ma an ce, kowa da irin kiwon da ya karbe shi, wai makwabcin mai Akuya ya sayi Kura.

Duk wata kasa mai cikakken 'yanci, wajibi ne tana da dokar tsaron kasarta. Kuma "Icce tun yana danye ake lankwasa shi". (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China