Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farashin man fetur ya tashi gabanin taron kungiyar OPEC
2020-06-03 11:29:54        cri

Farashin man fetur ya tashi, yayin da kasashe masu samar da man ke kokarin tsawaita rage yawan man da suke samarwa.

Mizanin farashin man na watan Yuli, na West Texas Intermediate, ya tashi da dala 1.37 inda ya tsaya kan dala 36.81 kan kowace ganga a kasuwar musaya ta New York Mercantile Exchange. Farashin da ya kasance mafi yawa tun bayan ranar 6 ga watan Maris, kamar yadda alkaluman kasuwar hannayen jari ta Dow Jones suka bayyana.

Mizanin farashin man fetur na Brent na watan Augusta, ya tashi da dala 1.25, inda ya tsaya kan dala 39.57 kan kowace ganga a kasuwar musaya ta London ICE.

An samu tashin farashin ne biyo bayan rahotannin dake cewa kungiyar kasashe masu samar da man fetur ta OPEC, da sauran kasashe masu samar da man, ciki har da Rasha, na tunanin tsawaita lokacin rage man da suke samarwa har ya zarce karshen watan Yuni, yayin taron da ake sa ran za su yi a gobe Alhamis. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China