Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tsawaita dokar hana fita a birnin New York har zuwa ranar Lahadi don magance aikata laifuka yayin da ake zanga-zanga
2020-06-03 11:09:08        cri
Magajin garin birnin New York na Amurka, Bill de Blasio, ya ce birnin zai ci gaba da kasancewa karkashin dokar takaita fita daga karfe 8 na dare zuwa 5 na safiyar washegari, har zuwa ranar Lahadi, da nufin magance aikata laifuffuka daga zanga-zangar da ake yi dangane da kisan George Floyd, Ba'amurke bakar fata.

Dokar da aka sanya ranar Litinin, wadda ita ce irinta na farko a birnin tun bayan shekarar 1943, ta fara aiki ne daga karfe 11 na dare, sai dai ba ta hana masu sace-sace fasa shaguna a Manhattan ba bayan gari ya yi duhu.

Rundunar 'yan sandan birnin ta ce an tsare sama da mutane 200 kafin dokar ta fara aiki ranar Lahadi da dare, inda a tsawon daren kuma aka tsare mutane sama da 700, galibinsu matasa.

Rundunar ta ce an ji wa wani jami'inta mummunan rauni, bayan wata mota ta buge shi tare da guduwa a yankin Bronx, yayin da aka kuma buge wani a Manhattan, lokacin da yake kokarin hana sata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China