Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompoe kalubale ne ga kasashen Turai
2020-06-02 21:20:03        cri

Duk da cewa, ana ta zanga-zanga a kai a kai a sassa daban daban dake fadin Amurka, amma sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, wanda akan kira da "sakataren harkokin wajen Amurka mafi karancin karfin aiki a tarihi" yana ci gaba da yin kariya domin yaudarar al'ummun kasashen duniya.

Kwanan baya yayin da yake zantawa da manema labaran gidan talibijin Fox, Pompeo ya yi kashedi ga kasashen Turai cewa, kasar Sin tana kawo barazana ga kasar Amurka, haka kuma tana kawo barazana ga kasashen yamma, don haka ya dace kasar Amurka da kasashen Turai sun hada kai domin yaki da kasar Sin.

Amma kullum kariya za ta kasance kariya ne kawai, ko da kuwa an maimaita sau dubu daya. Hakika kasashen Turai sun gano amfanin Pompeo, yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19 a fadin duniya, ba zai yiwu ba su amince da jita-jitar da yake bazawa, kuma bai kamata ba kasashen Turai su manta da cewa, 'yan siyasar Amurka sun taba dora laifi kan su bayan barkewar annobar, har ma sun taba kwace kayayyakin kiwon lafiyar da suka saya, kana sun bayyana cewa, 'yawancin masu dauke da cutar na Amurka sun zo ne daga kasashen Turai, inda suka hana 'yan asalin kasashen mambobin kungiyar tarayyar Turai shiga kasarsu, a karshe dai Amurka ta ki halartar babban taron samar da tallafin kudi domin yaki da annobar da kungiyar tarayyar Turai da kasashen da abin ya shafa suka shirya, daga matakan da 'yan siyasar Amurka suka dauka, ko ana iya ganin Amurka tana yin hadin kai da kasashen Turai?

Yanzu haka Amurka tana da wahalhalu a jere a cikin kasa, don haka Pompeo yana fatan kasashen Turai za su samar da taimako ga kasar Amurka, amma a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, masu zanga-zanga sun yi awon gaba da ofisoshin jakadancin kasar Amurka dake wakilci a kasashen Birtaniya, da Jamus, da Denmark da sauransu, inda suka nuna goyon baya ga zanga-zangar da ake gudanar a cikin Amurka, duk wadannan sun nuna cewa, babu hakkin bil Adama da 'yancin fadan ra'ayi a kasar ta Amurka.

Hakika abu ne mai sauki al'ummun kasashen Turai su gano wane ne abokinsu na gaske, kuma abun takaici ga al'ummun Amurka shi ne har yanzu, sakataren harkokin waje mafi karancin karfin aiki yana aiki a Amurka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China