Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fatan wasu yaran kasar Sin a ranar yara ta duniya
2020-06-01 15:03:54        cri
Malam bahaushe kan ce, yara manyan gobe. Yara suna bukatar a ba su kariya, tare da sauraran abun da suke fatan cimmawa. Albarkacin ranar yara ta duniya, wato ranar 1 ga watan Yuni, akwai wasu yaran kasar Sin wadanda suka bayyana fatansu.

Xu Huantong, wata yarinya ce daga birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin, inda a cewarta, tana fatan yin wasan filfilo a cikin yanayi mai kyau.

Liu Yanbo, wani yaro ne daga lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, inda ya ce fatansa shi ne a hanzarta dawo da harkokin karatu, domin yana son wasa tare da abokansa dake makaranta.

Har wa yau, wani yaro dan kabilar Yi daga birnin Leshan na lardin Sichuan ya ce, yana fatan zama mai samar da kek, saboda yana son cin kek sosai.

Sa'annan babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya gabatar da shirye-shirye masu kayatarwa domin taya daukacin yaran kasar murnar wannan rana.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China