Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude makarantu a jamhuriyar kasar Niger
2020-06-01 10:14:54        cri
Ma'aikatar ilimi ta jamhuriyar kasar Niger, ta ce jami'o'i da makarantun midil da na firamare za su bude daga yau Litinin, 1 ga watan Yuni, bisa la'akari da ingantuwar yanayin yaki da COVID-19 a kasar.

Haka zalika, gwamnatin kasar ta sanar ba gidajen rawa da na barasa a fadin kasar damar budewa.

Bisa alkaluman da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar jiya, an samun sabbin mutane 13 da aka tabbatar sun kamu da cutar a makon da ya gabata, inda mutane 3 suka mutu. Tun bayan bullar cutar a ranar 19 ga watan Maris, an yi wa mutane 4,708 gwajin cutar, inda aka tabbatar mutane 958 sun kamu, daga cikinsu, 839 sun warke, yayin 64 suka mutu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China