Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ficewa daga WHO zai lalata moriyar Amurka ita kanta
2020-05-31 20:50:48        cri

"Idan ba a biya bukatuna ba, zan fice daga hukumar" manufa ce da gwamnatin kasar Amurka take aiwatarwa a cikin 'yan shekarun da suka gabata, yanzu haka ana fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a fadin duniya, amma abun mamaki shi ne shugaban Amurka ya sanar da cewa, Amurka za ta yanke huldarta da hukumar lafiya ta duniya wato WHO, domin hukumar ba ta yi gyaran fuska bisa bukatar da Amurka ta gabatar mata ba, kana za ta juya akalar kudin tallafin da take baiwa hukumar zuwa ga wasu ayyukan na daban, matakin da Amurka ta dauka ya gamu da suka daga kasashen duniya.

Kwayar cuta ba ta la'akari da iyakar kasa, tana shafar daukacin kasashen duniya, muddin aka hada kai, to za a iya ganin bayan cutar daga dukkan fannoni, amma wasu 'yan siyasar Amurka ba su kula da kome ba sai hada-hadar kudi da takardun zabe, har sun dauki matakai uku a jere wato yin alkawari da dora larfi ga wasu da kuma yin kashedi, hakika duk wadannan sun jefa kasar ta Amurka cikin mawuyacin yanayi, yayin da suke dakile annobar, a karkashin irin wannan yanayi, 'yan siyasar Amurka sun dora laifi ga hukumar lafiya ta duniya wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta yayin dakile annobar a fadin duniya, da farko ta ki biyan kudin karo-karo, yanzu haka ta sanar da cewa, za ta fice daga hukumar, a bayyane an lura cewa, tana matsa lamba ga hukumar ne, kuma tana mayar da moriyar siyasar kanta a gaban yunkurin dakile annobar na al'ummun kasa da kasa, hakika tana lahanta hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren.

A matsayinta na hukumar kasa da kasa dake da kwarewa da gwarjini a fannin kiyaye tsaron kiwon lafiyar jama'a a fadin duniya, hukumar lafiya ta duniya tana taka babbar rawa yayin da kasashen duniya suke kokarin dakile annobar COVID-19, misali ta yi kashedin barkewar annobar ga daukacin kasashen duniya a kan lokaci, ta samar da shawarwari masu ma'ana kan yadda ake binciken kwayar cutar da yadda ake tantance mutunen da suka kamu da cutar, kuma ta samar da kayayyakin kiwon lafiya da maganin tantance kwayar cutar ga kasashe sama da 100, kana ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya daban daban domin samar da allurar rigakafi cikin sauri, ban da haka, ta kira babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa domin tsara shirin dakile annobar a fadin duniya, kokarin da hukumar take ya samu yabo daga al'ummun kasashen duniya baki daya.

Saboda haka kasashen duniya sun yi suka ga matakin ficewa daga hukumar da Amurka ta dauka, amma matakin ba zai kawo tasiri ga aikin hukumar lafiya ta duniya ba, amma matakin da 'yan siyasar Amurka masu son kai da tabuwar hankali suka dauka zai kawo hadari ga tsaron rayukan al'ummun kasar Amurka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China