Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman PMI na masana'antun kere-keren Sin ya ragu kadan a Mayu
2020-05-31 17:43:55        cri

Bisa ga alkaluman da hukumar kidddigar kasar Sin NBS ta fitar a yau Lahadi ya nuna cewa, alkaluman PMI na masana'antun kere-kere na kasar Sin ya ragu daga kashi 50.8% a watan Afrilu zuwa kashi 50.6 a watan Mayu.

Ayyukan kasuwanci a bangaren masana'antun kere-keren kasar Sin sun samu bunkasuwa a watan Mayu, duk da cewa karuwar ba ta kai ta watan jiya ba, in ji babban jami'in hukumar NBS, Zhao Qinghe.

A bisa ga binciken da aka gudanar game da kamfanoni, kashi 81.2% na kamfanonin sun samu bunkasuwar harkokin kasuwancinsu da kashi 80% tun bayan da aka dawo bakin aiki a watan Mayu.

Zhao ya ce, alkaluman da aka auna sun nuna cewa, an samu bunkasuwar sabbin odar kayayyakin sana'o'i 12 daga cikin sana'o'i 21 da aka bincike, lamarin da ya nuna an samu ingantuwar bukata a cikin gida.

Sakamakon annobar COVID-19, bukatun da ake samu daga ketare suna kara raguwa, inda alkaluman hukumar ta NBS ya nuna cewa, kawo yanzu, adadin bukatun ketare yana kan maki na 35.3.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China