Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutuwar wani dan asalin Afirka ya sake nuna ra'ayin kabilanci na Amurka
2020-05-30 20:51:53        cri

A kwanan nan, wani ba'amerika dan asalin Afirka ya rasa ransa sakamakon azabtarwar da wani dan sanda farin fata na kasar ya yi masa, al'amarin da ya haddasa tashin-tashina a sassa da dama na Amurka. A yayin da adadin mutanen da cutar COVID-19 ta hallaka ya zarce dubu 100 a kasar, wannan al'amarin ya tsananta halin da take ciki, har ma ya shaida ra'ayin wariyar launin fata da Amurka ke nunawa.

Lokacin da yanayin da ake ciki ke kara tsananta, shugaban Amurka ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa, masu tada zaune-tsaye ne suka yi rikici, har ma ya ce, idan aka ga 'yan fashi, a harbe su.

Nuna kabilanci ya dade yana addabar kasar Amurka. Bisa rahoton da aka bayar dangane da al'ummomin Amurka na shekara ta 2019, sama da kaso 40% na Amurkawa suna ganin cewa, ba'a samu ci gaba ba a fannin shimfida zaman adalci tsakanin al'ummomin kasar, har ma sama da rabin Amurkawa 'yan asalin Afirka na ganin cewa, ba zai yiwu a cimma burin shimfida adalci tsakanin al'ummomin Amurka ba.

Duk da cewa matsalar kabilanci ta dade tana addabar Amurka, amma 'yan siyasar kasar ba su yi tunani mai zurfi ba kan yadda za su iya tinkarar wannan matsala. A wani bangare, wasu 'yan siyasar kasar sun ayyana rikicin kabilanci a matsayin wani batun da ba za su iya tattaunawa kansa a fili ba, saboda a ganinsu, tattaunawa kan batun zai iya yin illa ga makomarsu. A dayan bangaren kuma, akwai wasu 'yan siyasar Amurka wadanda suka yi amfani da batun nuna bambancin kabilu domin hura wutar rikici da nemowa kansu moriya. Musamman a wannan lokacin da Amurka ke fuskantar yaduwar annobar COVID-19 mai tsanani, gwamnatin kasar ta dora alhaki kan al'ummomi marasa rinjaye, wadanda har kullum ake nuna musu wariyar launin fata.

Alkaluman kididdigar birnin New York sun yi nuni da cewa, zuwa ranar 26 ga watan Mayu, daga cikin mutane dubu 100, adadin 'yan asalin Latin Amurka gami da 'yan asalin Afirka wadanda suka kamu ko mutu sakamakon cutar COVID-19, sun zarce adadin fararen fata da suka harbu ko mutu sakamakon cutar. Kamar sharhin da jaridar Los Angeles Times ta wallafa kwanan nan, yaduwar annobar ta nuna cewa, gibin dake kasancewa tsakanin masu hannu da shuni da matalauta da kuma ra'ayin nuna wariyar launin fata na dada tsananta a Amurka. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China