Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ina hakkin Bil Adama a Amurka saboda ganin kisan wani bakar fata a Minnesota?
2020-05-30 15:40:35        cri

Duk duniya ta kalli wani faifan bidiyo da aka yada ta intanet, an ga yadda wani dan sanda ya danne wuyan wani mutum bakar fata, daga baya wannan mutumin ya mutu. Cikin bidiyon, da wani mutum dake tsaye ya dauka, an ga yadda dan sandan ya zuba gwiwoyin kafarsa a kan wuyan mutumin bakin fata har na mintoci 7 a lokacin da suka kama shi da yammacin ranar Litinin a Minneapolis, inda aka jiyo mutumin yana cewa "ba na iya yin numfashi", "don Allah ba na iya yin numfashi". Wannan ba kisan gilla ba ne? Wani irin laifin ya aikata har za a kashe shi ba tare da nuna wani tausayi ba?

Wannan mutum mai shekaru 46 a duniya, sunansa George Floyd, a cewar danginsa da kuma abokan aikinsa, shi mutum ne mai kirkiri amma ya rasa ransa a hannun 'yan sanda, bisa dalili amfani da kudin jabu. Sanarwar da sashen 'yan sandan jihar Minneapolis ya fitar ta ce, an gano mutumin yana da wasu matsalolin rashin lafiya, kuma jami'an 'yan sandan sun kira motar daukar marasa lafiya. Sai dai mutumin ya mutu jim kadan bayan kai shi asibiti. Hukumar FBI ta fara bincike game da mutuwar mutumin bakar fata.

An fusata sosai game da wannan lamari, har an yi zanga-zanga a wurin. 'yan sanda sun harba hayaki mai sa kwalla da harsashi mai haske da kuma harsashi mai kumfa.Wani mai zanga-zanga da ya yi karo da 'yan sanda ya ce, "Ina durkushe, na gabatar da wata alama ta zaman lafiya, amma 'yan sanda sun harbe min hayaki mai sa kwalla". To, ko da yaushe Amurka ta na ikirarin cewa ana kiyaye hakkokin Bil Adama a kasar sosai, har ta na zargi sauran kasashe da keta hakkin Bil Adama. To ga wannan al'amari, ko an ga kariyar hakkin Bil Adama a ciki?

Donald Trump ya ba da sako a kan Twitter cewa, FBI zai yi bincike kan lamarin, kuma za a tabbatar da adalci, muna ci gaba da sa ido kan lamarin ko za a baiwa bakaken fata hakkinsu.

A hakika dai, hakkin Bil Adama a Amurka na da fuska biyu, wasu Amurkawa suna da hakkin sosai, amma sauran al'umma fa, ba a ba da tabbaci kan wannan batu ba, ga misala:

A watan Fabrairu na shekarar bana, an harbi wani matashi Ahmaud Arbery dake zama a kudancin jihar Georgia a kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya je motsa jiki. Amma bayan watanni biyu an tsare wadanda suka aikata laifin.

Shekarar 2017, dan sanda ya kashe Justine Damond, saboda ta gabatar da rahoton cewa, mai yiwuwa an yi wa wata fyade a titin dake bayan gidanta. An hukunta wannan dan sanda da daurin shekara 12.5.

Shekarar 2016, dan sanda ya kashe Philando Castile, amma ba a yanke masa hukunci.

Shekarar 2015, ba a gurfanar da dan sandan da ya kashe Jamar Clark a Minneapolis ba.

Ran 17 ga watan Yuli na shekarar 2014, dan sanda a New York ya kashe Eric Garner mai talla a titi, saboda sayar da Sigari ba bisa doka ba.

Shekarar 2012, dan sanda ya kashe Trayvon Martin a unguwa George Zimmerman.

……

Dukkansu bakaken fata ne. Me ya faru ga hakkin bakaken fata a Amurka? Yaushe za a daina nuna bambancin launin fata? To, Donald Trump yana yunkuri neman zarce, kafin nan, ko zai iya warware wannan batu da kuma samar da cikakken tsaro ga al'ummar Amurkawa?

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China