Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko Ana Mutunta Hakkin Bil Adam Na Bakaken Fata A Amurka?
2020-05-29 13:04:36        cri

Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Amurka suka bayar a ranar 27 ga wata, an yi zanga-zanga tare da tayar da tarzoma a biranen Minneapolis and St. Paul a jihar Minnesota ta kasar tun daga ranar 26 ga wata. Don haka gwamnan jihar Tim Walz ya sa hannu kan wani umurnin jiha, inda ya sanar da dokar ta baci, tare da aikewa da sojoji don kwantar da kura a wurin.

A ranar 26 ga wata an kori jami'an 'yan sanda 4 a birnin na Minneapolis bayan wani mutum bakar fata ya mutu a hannunsu. A wani faifan bidiyo da aka yada ta intanet, an ga yadda dan sandan ya dora gwiwoyin kafarsa a kan wuyan mutumin bakin fata a lokacin da suka kama shi da yammacin ranar Litinin, inda aka jiyo mutumin yana cewa "ba na iya numfashi", "don Allah ba na iya numfashi". Sanarwar da sashen 'yan sandan jihar Minneapolis ya fitar ta ce, an gano mutumin yana da wasu matsalolin rashin lafiya, kuma jami'an 'yan sandan sun kira motar daukar marasa lafiya. Sai dai mutumin ya mutu jim kadan bayan kai shi asibiti. Dalilin da ya sa 'yan sandan kama shi shi ne, suna zarginsa da laifin amfani da dalar Amurka 20 na jabu.

Ko da yake kullum Amurka tana sukar sauran kasashen duniya da laifin keta hakkokin dan Adam a wasu fannoni, amma ita kanta ba ta ce komai ba, kuma ba ta dauki wani mataki dangane da kawar da nuna bambanci da wariya tsakanin al'ummomi ba. Nuna bambanci tsakanin mutane bisa hujjar addini, ko launin fata ya zama ruwan dare a kasar ta Amurka, duk da an hana yin haka bisa doka.

Kashe wani bakar fata da baya dauke da makami a fili, abin tsoro ne ainun. Amma irin wannan nuna bambanci tsakanin al'ummomi yana ta faruwa a Amurka. Me ya sa hakan ke faruwa? Saboda ra'ayin mulkin mallaka da kuma ba da kariya ga fararen fata bisa tsari, sa'an nan masu tsattsauran ra'ayin "mayar da muradun fararen fata gaba da komai" sun fara wannan aiki a matsayin 'yan sanda.

Amma ina ainihin dalilin da ya sa haka? A ganina, masu hannu da shuni na Amurka masu wayo ne, sun yi dabara don tabbatar da ganin ana tafiyar da harkokin Amurka bisa tunaninsu, kuma domin kiyaye muradunsu, su kan sanya batun launin fata kan wasu matsalolin zaman al'ummar kasa. Amurkawa bakaken fata ba su fahimci ainihin dalilin da ya sa ba su iya jin dadin zamansu ba, suna ganin cewa, dalilin shi ne an raina su, ana nuna musu bambanci saboda launin fatarsu, amma ainihin daliln shi ne tsarin jari-hujja da kuma tsarin da Amurka take bi wajen tafiyar da harkoki.

A ganina, korar 'yan sanda da jami'ai masu ruwa da tsaki za su kawo karshen tarzomar a Minnesota, amma ba za su ceci ran wannan bakar fata ba, kuma ba za su hana sake abkuwar irin wanann abin tausayi a Amurka a nan gaba ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China