Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane sama da 50 sun rasu sakamakon hare-hare a Congo Kinshasa
2020-05-28 13:24:34        cri

Wani jami'in kasar Congo(Kinshasa) ya gaskata a jiya Laraba cewa, cikin makon nan, an kai hare-hare da dama a yankin arewa maso gabashin kasar, wadanda suka haddasa rasuwar mutane sama da 50.

A wannan rana kuma, shugaban lardin Ituri ya bayyana cewa, kungiyar masu adawa da gwamnatin kasar Uganda ta ADF ta kai hare-hare sau da dama a lardinsa, sa'an nan, rundunar sojan kasar ta sanar da tura sojoji zuwa wurin domin kare fararen hula.

Tun lokacin da rundunar sojojin gwamnatin kasar Congo(Kinshasa) ta fara daukar matakan soja kan masu dauke da makamai ba bisa doka ba a yankin gabashin kasar a karshen watan Oktoban bara, sau da dama, kungiyar ADF ta kai hare-hare ga fararen hula domin maida martani.

Kungiyar ADF ta gudu zuwa yankin gabashin kasar Congo(Kinshasa) a shekarun 1990, sakamakon kashewar da sojojin gwamnatin kasar Uganda suka yi mata. Sa'an nan, a shekarar 2017, kungiyar ta sake kutsa kai, ban da wasu harkokin nuna adawa da gwamnatin kasar Uganda, haka kuma, ta kan kai hare-hare ga mazaunan wurin, da rundunar kiyaye tsaron kasar Congo(Kinshasa) da rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China