Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin Gwiwa Da Tsagaita Bude Wuta: Hanyoyin Shawo Kan Kalubalen Da Duniya Ke Fuskanta
2020-05-26 17:38:06        cri

 

Samun nasara kan kowanne kalubale na bukatar hadin kai da goyon bayan juna da kuma ajiye duk wani bambanci da sabani, musamman ma a irin wannan lokaci da duniya baki daya ta dukufa wajen yaki da annobar COVID-19 da bai ware launin fata ko kabila balle wata kasa ba.

A baya bayan nan ne sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a tsagaita bude wuta a duniya, domin samun nasara kan cutar.

A cewar hukumar lafiya ta duniya, kawo yanzu, annobar ta harbi mutane fiye da miliyan 5 da dubu 468 da wani abu, tare da hallaka fiye da dubu 345. Inda kuma har yanzu take ci gaba da cin karenta babu babbaka a manyan kasashe da ma kasashe masu tasowa, lamarin dake nuna cewa, ta zama abokiyar gaba ga dukkan al'ummar duniya.

Yayin da ake fama da wannan annoba, abu ne da ya dace a ce bangarori masu adawa da juna sun ajiye bambancin dake tsakaninsu domin hada hannu wajen ganin bayanta. Bisa la'akari da yadda tsarikan kiwon lafiya da yanayin zaman rayuwa suka tabarbare a kasashe masu fama da rikici, abu ne mai matukar wahala shawo kan cutar idan har ba a tsagaita bude wuta ba.

Baya ga haka, tun kafin barkewar cutar, fararen hula a irin wadannan wurare na cikin mawuyacin hali saboda rashin kayayyakin jin kai da kuma yadda ake take hakkokinsu. Durkushewar harkokin tattalin arziki da yanayin zaman rayuwa, zai kara jefa mutane masu rauni cikin halin ni 'yasu, idan har bangarorin dake rikici da juna ba su ajiye makamai sun hada hannu wajen ganin bayan wannan yanayi da ake ciki ba.

Ban da kara jefa fararen hula cikin mawuyacin hali, idan har aka ci gaba da bude wuta, to fatan da ake na shawo kan wannan annoba nan bada dadewa ba, zai zama tarihi. Saboda za ta ci gaba da yaduwa kamar wutar daji tare da halaka karin mutane, da durkusar da duk wani abu mai amfani ga rayuwar dan Adam.

Ko a makon da ya gabata, gidauniyar Tony Blair dake Birtaniya, ta nuna cewa, ayyukan 'yan ta'adda kamar na BH za su haifar da koma baya ga yunkurin da ake na ganin bayan annobar COVID-19.

Domin ayyukan nasu za su kara matsi kan ayyukan jinkai, da kara raba hankali gwamnatoci da hukumomi kan inda ya kamata su mayar da hankali, da kara jefa 'yan gudun hijra dake rayuwa cikin matsanancin yanayi, cikin karin matsin rayuwa.

 

Ya kamata a ce dan Adam ya dauki darasi daga barkewar wannan annoba, wadda ta nuna cewa babu bambanci a tsakanin al'ummar duniya baki daya bare kuma 'yan kasa daya da suke zaman 'yan uwan juna, wadda a lokaci guda, ta sanya duniya tsayawa wuri guda. A irin wannan lokaci fiye da ko yaushe, akwai bukatar karatun ta nutsu domin hada hannu wajen ganin an kyautata duniyar bil adama.

Babu wani alfanu ko abin alfahari da duniya ta samu daga yake-yake da tashe-tashen hankali, illa ma kara tagayyarata da suke yi da jefa al'ummarta cikin tsanani tare da asarar rayuka masu daraja.

Dole ne a wannan yanayi a samar da hanyoyin ceton rayuka da na warware sabani da shawo kan bambance-bambance domin shawo kan kalubalen dake gaban bil adama. Lokaci ne na hada hannu domin yaki da annobar da ta baibaye duniya.

A cewar Antonio Guterres, wannan yunkuri zai fara ne da ajiye makamai a ko'ina, yana mai cewa a yanzu, wannnan shi ne abun da bil adama suka fi bukata fiye da ko yaushe.

A cewarsa, "dole ne MDD ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a fannin ayyukan shirye-shiryenta na wanzar da zaman lafiya da hukumomin ayyukan agaji da taimakawa bangarori daban-daban na kasa da kasa da kwamitinta na sulhu da babban zaurenta, amma kuma, dole ne majalisar ta yi kira ga al'ummar duniya su matsawa gwamnatoci lamba, don tabbatar da an shawo kan wannan annoba, ba wai takaitata kawai ba, shawo kanta baki daya, domin magance tasirinta akan tattalin arziki da zamanta kewa".

Kiran nasa, na bukatar hada karfi da karfe tsakanin gwamnatoci da bangarorin adawa, da al'umma da bangarori masu rikici, da dukkan jama'ar duniya. Dole ne duniya ta zama tsintsiya madaurinki daya, muddun ana son samun ci gaba da zaman lafiyar da ake muradi. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China