Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan Da Sin Ta Dauka Sun Sa Kaimi Ga Kasa Da Kasa Wajen Yaki Da Cutar COVID-19
2020-05-19 19:33:14        cri

"Bari mu hada kai da juna domin kare rayuka da lafiyar al'ummomin kasashen duniya, da ma kare duniyarmu baki daya, a kokarin raya makomar bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya." Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wannan kira ne a yayin bikin bude babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 73, a daren jiya Litinin 18 ga wata agogon Beijing.

A yayin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19, Xi Jinping ya gabatar da fasahohin kandagarki da dakile yaduwar cutar a taron, inda ya ba da shawarwari guda shida ta fuskar karfafa aikin kandagarki, da kuma sanar da matakai guda biyar, domin inganta hadin gwiwar kasa da kasa kan aikin yaki da cutar COVID-19, lamarin da ya sa kaimi ga kasa da kasa wajen yaki da annobar, wadanda suka kuma samu goyon baya daga gamayyar kasa da kasa.

Gamayyar kasa da kasa sun nuna yabo ga kasar Sin, saboda taimakon da ta samar ga kasashen duniya. Shugaban babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 72, kana ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Laos Bounkong Syhavong, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi, ya sa kaimi gare su, ya kuma nuna goyon bayansa kan shawarar raya makomar bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya da Xi ya bayyana, yana kuma godiya matuka dangane da kokarin da kasar Sin ta yi wajen tallafawa dukkanin bil Adama.

A nasa bangare kuma, shehun malami a fannin harkokin siyasa na jami'ar Amurka ta Alkahira dake kasar Masar Noha Bakr ya ce, shawarar da shugaban kasar Sin ya bayar, game da kara ba da taimako ga kasashen Afirka ta burge shi sosai. Ya ce, ya kamata gamayyar kasa da kasa su yi koyi da kasar Sin a fannonin goyon bayan hukumar WHO, da goyon bayan hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da cutar COVID-19, da kuma taimakawa kasashe maso tasowa wajen yin kandagarki da dakile yaduwar wannan annoba.

Bugu da kari, kafar yada labarai ta Politico ta kasar Amurka, ta wallafa wani sharhi mai taken "A lokacin da kasar Amurka take kokarin zargin kowa da kowa, shugaban kasar Sin ya samar wa kasa da kasa fatan samun allurar rigakafi."

"A lokacin da muka hada kanmu, ba wanda zai hana mu." Babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana hakan yayin taron. Ya ce, a lokacin da ake yaki da cutar tsakanin kasa da kasa, kawai mu cimma nasarar wannan yaki ta hanyar hadin gwiwa, da kuma kawar da sabanin dake tsakanin bangarori daban daban, domin bauta wa babban burinmu na kare rayuka. Kamar yadda shugaba Xi ya bayyana, dukkanin bil Adama suna da makomar bai daya, kuma yin hadin gwiwa shi ne makami mafi karfi, a fannin cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China