Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sansanin gyaran jiragen sama mafi girma a Asiya ya fara aiki
2020-05-19 11:00:29        cri
Rahotanni daga kamfanin jiragen sama na China Southern, ya bayyana cewa, sansanin gyaran jiragen sama mafi girma a yankin Asiya, ya riga ya fara aiki, inda ya ke samar da hidima a sansanin gyara jiragen sama dake filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Daxing da ke birnin Beijing.

Matakin fara aiki da sabon sansanin gyaran jiragen saman, wani babban ci gaba a fannin dawowar harkokin kasuwanci. Shi dai wannan sansani, yana harabar kamfanin jiragen sama na China Southern a filin tashi da saukar jiragen sama na Daxing. Fadin sansanin ya kai kimanin mita dubu 40, ya kuma kunshi babban dakin gyara da wani gini mai hawa hudu dake hade da babban ginin.

Idan aka hade baki dayan sansanonin gyaran jiragen sama dake Asiya, wannan sansanin yana iya daukar manyan jiragen sama masu fadi guda uku da marasa fadi guda uku. Haka kuma ana iya gyara jiragen sama 12 a lokaci guda a ciki, wadanda suka hada da samfurin A380 guda biyu da B777 masu fadi guda uku.

Bugu da kari, ana iya gyara dukkan nau'o'in jiragen sama da suke da kowa ne irin matsaloli a cikinsa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China