Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko 'Yan Siyasar Amurka Suna yin kandagarkin Cutar, Ko kuma Suna Wasan Kwaikwayo ne?
2020-05-17 21:42:41        cri
Kwanan baya, an gabatar da karin labarai game da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, wadanda suka nuna mana yadda 'yan siyasan kasar Amurka suka yi karya kan wannan batu.

Cikin jawabin da ya gabatar a ranar 15 ga wata, Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana wajen wani taron manema labaru da ya gudana a ranar Juma'a da ta wuce cewa, kasarsa ta kaddamar da aikin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19 a ranar 11 ga watan Janairun bana. Sai dai an san cewa, kasar Sin ta bayar da bayanan tsarin kwayoyin cutar COVID-19 ga hukumar lafiyar duniya WHO a ranar 12 ga watan Janairu. Don haka idan kasar Amurka ta fara aikin binciken allurar rigakafi a ranar 11 ga watan Janairu, to, hakan na nufin kasar Amurka ta riga kasar Sin samu cikakken bayani kan kwayoyin cutar. Amma me ya sa, kasar Amurka ta boye wannan labari, har ma tana zargin kasar Sin cewar, wai Sin ta boye labarin da abin ya shafa?

Dangane da wannan lamari, al'ummomin kasa da kasa sun nuna shakku cewa, shugaban kasar Amurka ya ce, kasar ta fara yin nazari kan allurar rigakafi daga ranar 11 ga watan Janairu, amma, a baya, ya ce, bai taba jin labarin cutar COVID-19 ba har zuwa karshen watan Janairu, wane labari ya zama gaskiya, kuma wane ne ya kasance karya? Kana, idan kasar Amurka ta riga ta fara yin nazari kan allurar rigakafi daga ranar 11 ga watan Janairu, me ya sa, kasar ta fara daukar matakan dakile yaduwar cutar har zuwa ranar 13 ga watan Maris? Ko 'yan siyasan kasar Amurka suna yin karya kan wannan batu ne?

Lamarin da ya sa, ana ganin cewa, cutar ta barke a kasar Amurka kafin lokacin da gwamnatin kasar ta gabatar. A hakika dai, a watan Maris na bana, shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka Robert Redfield ya gaskata cewa, akwai mutanen da suka rasu sakamakon cutar numfashi ta COVID-19, wadanda aka yi zaton sun rasu sakamakon mura mai yaduwa. Sa'an nan, a karshen watan Afrilu, magajin garin Belville na jihar New Jersey Michael Melham ya ce, ya taba kamuwa da cutar a watan Nuwanba na bara. Lamarin da ya sa, an fara yin shakku kan lokacin faruwar cutar numfashi ta COVID-19.

Ya zuwa yanzu, mutane sama da dubu 90 sun rasa rayukansu sanadiyyar annobar, yadda 'yan siyasa na kasar Amurka za su ci gaba da karyarsu? (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China