Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Abin da faru a yau ya taba faruwa shekaru sama da dari da suka wuce
2020-05-16 21:33:19        cri
Jama'a, shin me kuka sani game da "Spanish flu", shin cuta ce da ta samo asali a kasar Spaniya? A hakika, abin da ya faru a yau kusan ma ya faru a sama da shekaru dari da suka wuce.

A farkon shekarar 1918, lokacin da ake dab da kawo karshen yakin duniya na farko, mummunar cutar nan da daga bisani aka yi mata suna da "Spanish flu" ta fara addabar kasashen duniya. A cikin watanni uku kadai, cutar ta yadu zuwa duk fadin duniya, wadda har ta hallaka mutane kimain miliyan 20 zuwa miliyan 50, wasu har sun kiyasta cewa mutane sama da miliyan 100 sun mutu, adadin da ya zarce yawan mutanen da suka mutu a sakamakon yakin duniya na farko.

Sai dai cutar ta fara bulla ne a wani sansanin soja da ke jihar Kansas ta kasar Amurka a maimakon kasar Spaniya. Da farkon fari, wani kuku ne ya fara nuna alamun cutar, kafin daga bisani sojoji sama da 500 su harbu da cutar cikin kwanaki kalilan. Daga baya, an gano bullar cutar a sauran biranen Amurka.

A watan Maris na wannan shekara, sojojin Amurka dubu 84 sun shiga jirgin ruwa zuwa Turai, adadin da ya karu zuwa dubu 118 ya zuwa watan Afrilu.

Duk da cewa ci gaban harkokin zirga-zirga a wancan zamani bai kai na yanzu ba, amma cutar ta yadu cikin sauri zuwa akasarin kasashen duniya, ciki har da Birtaniya da Faransa da Jamus da Italiya da Spaniya da Rasha da Sin da Japan da sauransu, lamarin da ya nuna cewa, cuta ba ta san kasa ba, kuma ba ta san kabila ba.

To, amma shin me ya sa aka ma cutar lakabin "Spanish Flu"? Ashe, a lokacin, kasar Spaniya ta sha munanan hasarorin cutar. Kimanin kaso daya bisa uku na al'ummar kasar sun kamu da cutar, har ma sarkin kasar a zamanin ya harbu da cutar. Kasar Amurka a wancan lokacin da ke yakin duniya domin karfafa gwiwar sojojinta ba ta ba da labarai sosai a kan cutar ba, a yayin da kafofin yada labarai na kasar Spaniya suka samar da rahotannin yaduwar cutar a kasar ba tare da rufa rufa ba, matakin da ya sa ba da jimawa ba sauran kasashen duniya suka fara kiran cutar da "Spanish flu", duk da rashin amincewar da Spaniya ta nuna, kuma har yanzu ana kira cutar da sunan "Spanish flu". To, kun ga abin da ya faru ga mai fadin gaskiya.

A ganin wasu kasashen, tabbas cutar ta zo ne daga makiyayya. A lokacin, Amurka na gwabza fada da Jamus, don haka, kafofin yada labarai na Amurka ma su kan alakanta cutar da mutanen kasar ta Jamus.

Shekaru sama da dari sun wuce, hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta fitar da ka'idar lakabawa cututtuka suna, inda ta bukaci a guji alakanta cutuka da wata kasa ko wata kabila ko kuma wata sana'a. Ta kuma ba da shawarar kada a yi wa wata cuta lakabi da sunan wata kasa. Hakan ya faru ne a sakamakon yadda al'umma suka fara gane cewa, akwai matsalolin da ke tattare da alakanta wata cuta da wata kasa. A sa'i daya, hakan babu adalci da martabawa ga kasar, a waje guda kuma, ba zai taimaka ga dan Adam gudanar da nazari kan cutar ba.

Bayan barkewar cutar Covid-19, sau tari wasu 'yan siyasar Amurka sun yi ta alakanta cutar da kasar Sin, har ma sun kira cutar da "China Virus", matakin da ba ma kawai ya jawo suka daga bangaren kasar Sin ba, har ma da masu idon basira na kasar ta Amurka.

Sanin kowa ne gwamnatin Amurka na shafa wa kasar Sin bakin fenti ne don boye gazawarta wajen daukar matakan da suka dace na tinkarar cutar, lamarin da ya sa kawo yanzu yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai sama da miliyan 1.4, a yayin da yawan mamata a sanadin cutar ya zarce dubu 80 a kasar. To, tambaya a nan ita ce, kasancewar Amurka kasar da ta fi ci gaban harkokin kiwon lafiya a duniya, shin me ya sa ta zama kasar da ta fi samun mutanen da suka harbu da cutar da kuma mutuwa a sakamakon cutar?

Duk da cewa, an fara ba da labarin cutar Covid-19 a kasar Sin, amma ko da gaske ne cutar ta samu asali a kasar, har yanzu ta kasance tambaya, wanda aiki ne da ya kamata a dora wa masu nazarin kimiyya a maimakon 'yan siyasa.

Shekaru dari da suka wuce sun samar mana gaskiyar lamarin da ya faru a yayin yaduwar cutar "Spanish Flu". Amma ko akwai sauran abubuwan da muka karu da su cikin shekaru dari da suka wuce? Lalle ban da ci gaban harkokin kiwon lafiya da kimiyya, akwai kuma darasi da muka koya daga tarihi, wanda kuma zai samar mana idon basira.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China