Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ba za ta hana harkokin nazarin sararin samaniya na kasar Sin ba
2020-05-09 19:48:16        cri

A halin yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 na yin sauki sosai a duk fadin kasar Sin, kuma zaman rayuwar al'ummar kasar, gami da harkokin bangarori daban-daban na samun murmurewa yadda ya kamata, ciki har da harkokin nazarin kimiyya da fasaha.

A ranar Talatar da ta gabata, Sin ta harba sabon kumbo na gwaji maras dauke da mutane, ta amfani da rokar Long March-5B, daga tashar harba kumbuna dake Wenchang, tashar dake lardin Hainan a kudancin kasar ta Sin. Harba rokar dai ya kasance mataki na 3, a jerin ayyukan sama jannati da kasar ke gudanarwa, ayyukan da suka kunshi gina tashar samaniya mallakar Sin.

A cewar hukumar lura da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA a takaice, karkashin shirin kasar na fara amfani da sabuwar rokar, Long March-5B zai gudanar da aikin safarar kayayyakin da ake bukata, don kafa tashar samaniya ta Sin.

A wata sabuwa kuma, sashen matuka na kumbon 'yan saman jannati masu aikin gwaje gwaje na Sin, ya dawo doron duniya cikin nasara a jiya Jumma'a. Sundukin ya sauka ne a tashar Dongfeng dake jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kansa, a arewacin kasar ta Sin, da karfe 2 saura mintuna 11 na ranar jiya, bisa agogon Beijing.

Hukumar CMSA mai lura da harkokin sama jannati ta kasar Sin ce ta tabbatar da lamarin. Ta kuma ce, kumbon na gwaji ya shafe kwanaki 2 da sa'o'i 19 cikin falakinsa, inda a lokacin ya gudanar da wasu gwaje-gwajen kimiyya da fasaha masu nasaba da binciken sararin samaniya.

Dawowar sashen matuka na kumbon 'yan saman jannati doron duniyarmu, wata babbar nasara ce da kasar Sin ta samu a fannin binciken duniyar wata, da tafiyar da harkokin tashoshin sararin samaniya, musamman a daidai wannan lokaci na yakar cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin kasar Sin, nasarar da ta karfafawa al'ummar kasar gwiwa sosai.

Tun shekara ta 1992 zuwa yanzu, wato bayan da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tsara wasu muhimman matakai uku da kasar za ta bi, domin tura 'yan saman jannatinta zuwa sararin samaniya, sau 16 ke nan kasar na tura kumbunan dan Adam zuwa sararin samaniyar, har ma akwai 'yan saman jannati 11, wadanda suka taba yin tafiya a sararin samaniyar. Ke nan hakan na nufin an kammala ayyuka mataki na farko da na biyu, saura sai na uku.

Binciken sararin samaniya, wani jan aiki ne a gaban kowace kasa, wanda ba shi da iyaka kuma babu tsayawa, musamman fannin tura 'yan saman jannati zuwa sararin samaniyar. A duniyar wata kuma, akwai albarkatu masu tarin yawa, wadanda manyan kasashen duniya ke kokarin gudanar da bincike a kansu, ciki har da Amurka da Sin.

Duk da cewa ita Amurka ta tura 'yan saman jannatinta zuwa duniyar wata tun tuni, amma kasar Sin ba ta taba dakatar da kokarinta a wannan fanni ba, har ma tana taimakawa sauran wasu kasashen duniya, ciki har da Najeriya, a fannin harba taurarin dan Adam zuwa sararin samaniya.

Kamar yadda al'ummar kasar Sin ke zama tsintsiya madaurinki daya, wajen dakile yaduwar cutar COVID-19, masana kimiyyar kasar ma suna ta namijin kokari, domin harhada magani gami da samar da allurar rigakafin cutar. Al'ummar kasar Sin ba su taba yin kasa a gwiwa ba, duk da cewa akwai manyan kalubaloli ko hadurra a gabansu, haka aikin binciken sararin samaniya yake.

Binciken sararin samaniya zai taimaka sosai ga lalubo sabuwar hanyar bunkasa tattalin arziki, da yin amfani da albarkatu iri daban-daban dake tattare da sararin samaniyar, har ma akwai yiwuwar zai canja zaman rayuwar dan Adam baki daya a nan gaba, shi ya sa kasar Sin ba za ta tsaya a baya ba a wannan fanni, kana, za ta ci gaba da nuna kwazo tare da sauran kasashen duniya, domin bayar da gudummawa gwargwadon karfinta, ga ci gaban al'ummar fadin duniya baki daya. (Murtala Zhang)
 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China