Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwar kasa da kasa ne kawai zai rage radadin COVID-19
2020-05-07 19:29:13        cri

Cutar numfashi ta COVID-19 da a yanzu haka ke addabar sassan duniya, ta haifar da kalubale masu tarin yawa. Yayin da masana ke kallon ta a matsayin cutar da tasirin ta ka iya jimawa ana jin radadin sa. To sai dai kuma a daya hannun, mafi rinjayen tunani na masana, da masu ruwa da tsaki a yakin da ake yi da wannan annoba, na ganin ba wata dabara da ta wuce hada kai waje guda, tsakanin dukkannin sassan duniya a mataki na kasa da kasa, wajen aiwatar da matakan kawar da wannan cuta da za su amfani kowa.

Wasu daga cikin muhimman fannonin da wannan cuta ta yiwa mummunan tasiri su ne fannonin kiwon lafiya, tattalin arziki, farfadowar ayyukan masana'antu, da dai sauran su.

Idan mun dubi fannin lafiya, za mu ga cewa, duniya ta shiga wani mawuyacin hali sakamakon bullar wannan cuta, an yi asarar rayukan mutane sama da 260,000, yayin da adadin wadanda suka harbu da wannan cuta ya haura miliyan 3 da dubu 800. Wadannan alkaluma na ci gaba da karuwa, yayin da kwararru a fannin likitanci ke ci gaba da kokarin bincike, domin samar da alluran riga kafin cutar ta COVID-19, wadda wasu ke hasashen na iya kaiwa shekara guda kafin samuwar ta.

Duba da wannan yanayi, abun da yake wajibi a nan shi ne, karfafa hadin gwiwa wajen inganta irin wadannan ayyuka na gwaje gwaje, tsakanin masana na kasa da kasa, ko a kai ga cimma nasarar da aka sanya gaba. Sabanin abun da muke gani a yanzu, inda wasu 'yan siyasa musamman na wasu kasashen yammacin duniya, ke mayar da wannan batu hanyar yayata manufofi na siyasa.

Mun dai ga yadda a irin wannan yanayi kasar Sin, ke ta samar da tallafi na kayayyakin kiwon lafiya masu nasaba da ba da kariya, da kandagarkin yaduwar wannan cuta ga kasashen duniya daban daban, a wani mataki na sauke nauyin dake wuyan ta, na tallafawa yaki da wannan annoba daga dukkanin fannoni. Matakin da ko shakka ba bu ya cancanci yabo. Musamman idan aka yi duba da cewa, wasu kasashe masu tasowa dake karbar irin wannan taimako na kasar Sin, ba su da karfin magance wannan kalubale na lafiya da kan su.

Gaba ta biyu ita ce batun tattalin arziki. A nan sanin kowa ne cewa, wannan annoba ta COVID-19 ta riski kasashen duniya da dama ba zato ba tsammani, lamarin da ya haifar da gagarumin koma baya a fannin tattalin arzikin su. Kamfanonin sun rufe, al'ummu da yawa sun rasa dama ta ayyukan yi, kana wasu masana'antun sun durkushe. An ma yi hasashen cewa, ko bayan wannan annoba, da yawa daga kamfanoni manya da kanana ba za su iya farfadowa ba. A irin wannan gaba, babban abun da kasashen duniya ke bukata shi ne hadin gwiwa da fahimtar juna, tare da daukar matakan da za su saukakawa kasashe, musamman masu raunin tattalin arziki radadin da za su sha, kasamakon wannan yanayi.

Cikin muhimman matakai da tuni kasashe irin Sin suka dauka, shi ne jinkirta lokacin biyan basussuka da suke bin kasashe masu tasowa, baya ga dage lokacin biyan wasu basussukan da bankuna ke bin masu kanana da matsakaitan kamfanonin dake cikin gida. Hakika hakan ya nuna irin fahimta da Sin ke da ita, game da matakan raya tattalin arziki a gida da waje, musamman a irin wannan lokaci da ake ta kokarin magance yaduwar wannan annoba, da kuma farfadowa harkokin raya tattalin arzikin duniya.

Batun komawa hada hadar cinikayya, da kasuwanci na da matukar muhimmanci, duba da cewa sassan duniya na dogaro da juna wajen ko dai samar da kayayyakin da ake bukata domin sarrafawa a masana'antu, ko kuma hajojin da masana'antun ke samarwa domin masu sayayya. Don haka nauyi ne babban kan dukkanin kasashen duniya, na su samar da dabarun komo da harkokin cinikayya, musamman a gabar da manyan kasashen dake kan gaba wajen karfin tattalin arziki a duniya wato Sin a Amurka, ke ci gaba da gogayya da muka takara a fannin. Wannan mataki kari ne kai bukatar hadin gwiwa tsakanin manyan kasashen duniya masu fada a ji, na tunkarar duk wata annoba daka iya fuskantar duniya nan gaba a kan lokaci, ba kuma tare da wata rufa rufa ba.

Wannan kuwa shi zai kai mu ga tambayar kan mu, muhimman batutuwa da dama, kamar wadanne matakai ne za a bi domin farfado da ayyukan masana'antu da harkokin ba da hidima? Ta yaya za a kai ga warware matsalolin kudi da nan kasuwanci da wannan annoba ta COVID-19 ta haifarwa duniya, ciki hadda dunbin basussuka da ake bin kasashe daban daban? Da ma batun wadanne hanyoyi za a bi domin warware kalubalen daraja da cinikayyar makamashi kamar danyen mai, da suka bijiro sakamakon bullar wannan annoba? Ko shakka babu hadin kai tsakanin kasashen duniya, a nan ma shi ne dai mafita, idan har kasa da kasa na fatan ganin an gudu tare an tsira tare!!!!!!!!!!!

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China