Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana wata Ga Wata…
2020-05-06 16:37:06        cri

A yayin da duniya ke fama da annobar COVID-19, a hannun guda kuma babban darektan shirin samar da abinci na duniya (WFP) David Beasley, ya yi gargadi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya. Wai ana maganar targade sai ga karaya" Jami'in ya ce, ai ya fadawa shugabannin kasashen duniya yayin wata tattaunawar da suka yi watanni da dama da suka gabata, kafin ma cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, a shekarar 2020 da muke ciki, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu saboda wasu dalilai. Abin da malam bahaushe ke cewa, duk wanda bai ji gari ba, to kuwa zai ji hoho."

Amma duk da wannan babbar matsala da aka yi hasashen za ta kunno kai, Beasley ya shaidawa zaman muhawarar kwamitin sulhu kan yadda za a kare fararen hula da yunwa ta shafa sakamakon rikici cewa, yayin da ake fama da COVID-19, "Ina son in jaddada cewa, ba kawai muna fama da annobar lafiya da ta shafi duniya baki daya ba, har ma ta haifar matsalar jin kai."

Jami'in ya ba da misali da wani sabon rahoto da aka fitar game da matsalar abinci da duniya ke fuskanta, inda ya nuna cewa, kimanin mutane miliyan 821 ne suke kwana da yunwa a duniya. Akwai kuma karin mutane miliyan 135 dake fama da matsalar yanayi na yunwa ko fiye da haka. 
 

Wani sharhin da shirin na WFP ya fitar, ya nuna cewa, a sakamakon annobar COVID-19, ya zuwa karshen shekarar 2020, wasu karin mutane miliyan 130 za su iya fadawa kangin yunwa, yayin da adadin mutanen da za su fuskanci babbar matsalar karancin abinci a fadin duniya, zai karu zuwa miliyan 265. Kuma ra'ayin ba da kariya zai tsananta matsalar.

Rahoton baya-bayan nan da shirin na WFP ya fitar ya bayyana cewa, daga cikin mutane sama da miliyan 100 dake fuskantar matsalar rashin abinci, akwai sama da miliyan 70 a nahiyar Afirka. Baya ga tarin matsalolin da muka ambata a baya, fadace-fadace sama da dubu 20 da ake ganin sun barke a bara a nahiyar Afirka, su ma sun tilasta jama'a barin muhallansu, da kawo tsaiko ga ayyukan noma da samar da abinci. Har wa yau, wasu iftila'i ciki har da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa da fari, sun sa mutane a kalla miliyan 33 cikin matsalar rashin abinci, ga kuma matsalar farin dango dake addabar gabashin Afirka ta jefa miliyoyin al'umma cikin hadari. Wannan shi ne wai, ana dara ga dare ya yi.

A yankin kahon Afirka dake gabashin nahiyar kuma, akwai makaurata sama da miliyan 6 da 'yan gudun hijira fiye da miliyan 3. Haka kuma akwai wasu miliyoyin al'umma wadanda suke cikin akuba sakamakon bala'un ambaliyar ruwa ko fari. Wannan ita ce aljannar Waina, sama zafi kasa zafi". Ga matsalar COVID-19, ga kuma wasu matsaloli dake kara kunno kai.

Abun da ya fi muhimmanci yanzu shi ne ci gaba da tallafawa irin wadannan mutane da suka shiga irin wadannan matsaloli. Yanzu haka, yaduwar annobar COVID-19 tana haifar da kalubale ga gwamnatocin kasashe daban-daban daga dukkan fannoni, wato daga bangaren lafiyar al'umma, zuwa kawar da talauci da samar da guraban ayyukan yi da isasshen abinci. Duk da cewa kasashe daban-daban a Afirka sun rufe iyakokinsu, amma suna ci gaba da karfafa hadin-gwiwa domin tabbatar da musanyar manyan hajoji tsakaninsu. Da ma, ai hannu daya ba ya daukar jinka.

Baya ga matsaloli na rashin abinci da guraben ayyukan yi da ma kudin shiga da matsalar COVID-19 ta haifar ga duniya, shi ma bankin duniya ya yi hasashen cewa, za a samu raguwar kudaden da suka kai dala biliyan 37, kimanin kaso 23.1 cikin 100 a kasashen Afirka dake yankin kudu da hamadar Sahara a shekarar 2020 da muke ciki, sakamakon matsalar tattalin arziki da cutar COVID-19 ta haifar gami da rufe wuraren ayyukan yi.

Bankin ya ce, yayin da ake hasashen kaso 4 cikin 100 na al'amura za su farfado a shekarar 2021, a hannu guda kuma, al'amura za su sake komawa baya, saboda raguwar kudaden shiga da ayyukan yi da ma'aikata 'yan ci-rani za su fuskanta, matakin da zai kara haifar da rasa ayyukan yi da kudin shiga sakamakon matsalar tattalin arziki a kasashen da suke zama. Komai ya yi zafi, aka ce maganinsa Allah.
Yayin da duniya ke kara koyon darussa da dama daga COVID-19, lokaci ya yi da za a karkata ga tunanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, wato gina kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. Kukan kurciya jawabi ne, amma mai hankali ne kadai ya ke ganewa. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China