Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo ya kara fitar da jita-jita a gaban kimiyya
2020-05-04 20:26:46        cri

A gaban sakamakon da masanan duniya baki daya suka samu game da cutar COVID-19, cewa cutar ta samo asali ne daga halittu, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo a jiya Lahadi, a yayin da yake zantawa da kafofin watsa labaru, ya kara ambatar jita-jitar da ya yi a baya, cewa wai "Abubuwan shaidu masu yawa sun nuna cewa, cutar ta samo asali ne daga cibiyar gwaji ta Wuhan".

Ban da wannan kuma, kwanan baya shugaban kasar Amurka, shi ma ya bayyana a taron manema labarun na fadar White House, cewa, wai ya taba ganin "abubuwan shaidun dake tabbatar da asalin cutar COVID-19 daga cibiyar gwaji ta kasar Sin ta fito". Amma, game da ra'ayin dake kunshe a cikin sanarwar ofishin kwamishinan lekan asiri na kasar ta Amurka, cewa "cutar COVID-19 ba dan Adam ne ya kirkire ta ba, kuma ba a taba yin gyare-gyare kan kwayar hallitunta ba", shugaban na Amurka bai iya ba da amsa kan dalilin da ya sa har yanzu, yake nuna shakku kan cibiyar binciken cututtuka ta Wuhan ba.

A hakika dai, tun farkon farawa, masana a fannin kimiyya da kiwon lafiya na kasa da kasa, sun musunta makircin da ake yi game da asalin cutar cewa daga cibiyar gwaji take, "Cutar hadari ce na halitta" wannan ya riga ya kasance ra'ayin bai daya na kasashen duniya. Kana ya samu goyon baya daga hukumar WHO, da hukumar nazari ta Pasteur ta kasar Faransa, da kuma wasu kwararru da masana, ciki har da furofesa Ian Lipkin na jami'ar Columbia, wanda ake kiransa "mafaraucin cututtuka".

 

Kwanan baya, Tasuku Honju, wanda ya samu kyautar karramawa ta MDD ta Nobel kan ilmin yadda jikin halittu ke aiki ko likitanci, kuma masanin dabarun dakile kamuwa da cutuka na kasar Japan, shi ma ya wallafa sharhi, na zargin mugun aikin da wasu mutane suka yi, na yada jita-jita ta hanyar amfani da sunansa.

Ya zuwa ranar 4 ga watan Mayu, da misalin karfe 5 na safe bisa agogon Beijing, cutar COVID-19 ta riga ta haddasa rasuwar Amurkawa sama da dubu 66, inda adadin ya wuce yawan sojojin Amurka da suka mutu a lokacin yakin Vietnam. Ana ta kara lahanta al'ummar kasar ta Amurka. Amma, domin biyan bukatunsu kan babban zabe, Mike Pompeo da sauran wasu 'yan siyasa, ba sa bincikar kansu, game da matakan dakile cutar a kasar, da kuma ba da amsa kan shakkun da jama'ar kasar suka nuna musu ba, a maimakon haka, suna amfani da yaduwar annobar don kara fitar da jita-jita iri daban daban kan kasar Sin, don karkatar da hankalin al'umma, game da rashin gamsuwa da suke nunawa, kan yadda gwamnatin kasar ta yi sakaci, wajen aikinta na dakile cutar.

Mike Pompeo da makamantansa, ba su ji kuma ba su ganin shakku masu dacewa da aka nuna musu, game da ayyukansu na dakile annobar. Amma abun tambaya a nan shi ne, ko me ya sa aka dakatar da ayyukan cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa ta sojojin kasa na kasar kan nazari a wasu fannoni ba zato ba tsammani?

A cikin wadanda suka kamu da mura mai yaduwa a kasar, nawa ne a hakika suka kamu da cutar COVID-19? Yaushe ne aka soma yada cutar a tsakanin al'ummomin kasar? Me ya sa fadar White House ta yi kokarin hana shahararren masanin cututtuka masu yaduwa Anthony Fauci, ya ba da shaidu a majalisar wakilan kasar? ……Gaskiya dai har yanzu Mike Pompeo da masu mara masa baya, ba su yi wani bayani ba ga jama'ar kasar Amurka da ma kasashen duniya.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China