Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata mulkin Trump ya ji kunya ya gagara yin fada da chutan Korona
2020-05-04 14:32:52        cri
By Aliyu Sawa

Akwai jita-jita game da China a kan Chiwon Covid 19 har ya sa mutane da yawa suna chewa a kira China ga doka. Sabi da haka Shugaban Kasar Amerika ke ta kiran covid-19 da sunan "Chutan China".

Gaskiyan shi ne mulkin Trump ya gagara yin fada da chutan nan, kuma yana jin kunya inda zai yadda wai ya gagare shi.

Na ba da gaskiya chewa, sa wa China laifi kawai, hanya ne, ta jan hankalin mutane daga gaskiya, wanda shi ne gomnatin kashashe da yawa sun kasa yin abun da ya kamata don hana yaduwar Corona Virus a kasashen su. Ya kamata kowa ya rike gwamnatin kasan sa da laifin.

Misali, bayan da kwayar cutar ta fara yaduwa a wajen kasar China, sai kungiyar kimiyya ta yi kararrawa, kuma yawancin ma'aikatan gwamnatin Amurka ba su dauke shi da zafi ba don shugaban Amurka da kansa ya rage gaskiyan hadarin ciwon. wannan kuma za a ce laifin China ne?

Kamar yadda mu 'yan Nijeriya muka yi watsi da kokarin da China ke yi wajen yakar da chuta nan da ba wanda ya san akwai shi kamun yanzu.

Shekaru da shekaru muna ta jin duk abun da kudu ta gaya mana, a wannan yawan shekarun, me muka kulla. suna ta amfani da mu don tsiyasa kawai.

Ya kamata mu fara tunani ma kan mu, mu fada ma kan mu gaskiya, tsiyasan duniya ba taimakon mu za ta yi ba.

Duniya na iya tunanin cewa a cikin makonnin farko na yaddawar cutar a watan Disamba da Janairu, hukumomin Wuhan sun ja jiki da rahoto game da kamuwa da cutar, wanda ya sa an kasa daukan matakan magance shi da sauri.

Amma bai kamata mu manta cewa dole ne ku san abin da ya same ku kafin ku iya ɗaukar matakai, a wannan yanayin ba a san cutar ba, saboda haka zai zama da wuya a faɗi abin da ba a sani ba.

Na ba da gaskiya cewa China ta yi kokari sosai ta wajen kokarin hana yaduwar wannan ƙwayar cuta mai ban mamaki.

Dukkan mu ba za mu musanta cewa, a cikin January, China ta kulle garin da aka fara sanin da ciwon, Wuhan, ta hana shiga da fitowa a garin, ta hana mutanen ta yawo ma a cikin gari saboda kokarin hana yaduwar ciwon.

Masanan kasar China sun yi bala'in kokari da suka gane kan cutar da sauri, ta haka sauran kasashe suka samu labari da gane kan ciwon, da ba su yi kokari sun gane ba fa? Me zai faru?

Ko mun ki, ko mun so, yanzu China ne masu kwarewa da ilimin yakar da wannan abin.

Yan China a shirye suke don sun taimaka a kowace hanya da za su iya taimakawa, idan kawai za mu iya mu manta da jita-jita da ba gaskiya da tunanin da ba su da tushe, za mu gan gaskiya a fili, shi gaskiyan nan kuma zai taimake mu yaki da wannan Covid-19 don cheton ran dan adam.

Kar mu manta cewa, Kwayar cuta ta Corona Virus ba ta san wani launin fata, aji, gari, ko addini ba, dole ne mu manta da duk wata damuwa da siyasan duniya ke kawowa don mu hada kai wajen yaki da wannan bazan ciwo da ake kira corona virus, in ba haka ba, dan adam na cikin wani hali.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China