Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shin Sabuwar Cutar Coronavirus An Kirkire Ta A Dakin Gwaje-gwaje Ne? Ta Yaya Hakan Ya Faru? Wasu Dalilai Hudu Daga Masanan Kwayoyin Cutuka Na Amurka
2020-05-03 22:00:49        cri

Jonna Mazet, wata kwararriya a fannin nazarin cutukan dake yaduwa a tsakanin al'umma a reshin Davis na jami'ar California, wadda ta yi aikin bada horo da kuma yin hadin gwiwa da kwararrun masu bincike daga cibiyar nazarin kwayoyin cutuka ta Wuhan, ta ce akwai kyakkyawan tsammanin cewa sabuwar cutar coronavirus ba kirkirar ta aka yi a dakin gwaje gwaje ba bisa wasu manyan dalilai hudu.

 

Bayanin ya nuna cewa, bayan da tawagar Joana mazet suka tattara rahoto kan sabuwar cutar coronavirus, Shi Zhengli, wata masaniyar cibiyar nazarin cutuka ta Wuhan wadda ta taba yin aiki tare da ita a lokacin baya, ta yi gaggawar duba gwaje gwajen da aka yi, kuma sai ta kwatanta bayanan da aka samar game da sabuwar cutar coronavirus tare da sauran kwayoyin cutuka wanda tawagar ta samu daga jikin jemagu, sai ta gane cewa ba su dace da juna ba.

 

 

Dalili na 2: dakin gwaje gwajen ya yi amfani da tsauraran matakai wadanda Mazet ta gabatar cewa akwai shakku game da ingancin cibiyar nazarin cutuka ta Wuhan(wiv), amma ta yi amanna cewa aikin da kwararun masu binciken kasar Sin suka gudanar ya wuce a yi watsi dashi, koda a dakin gwaje gwaje ne ko kuma a wajen daukar samfuri ne.

 

Dalili na 3: sabuwar cutar coronavirus ita ce kwayar cutar mafi sabunta da ake dauka daga jikin dabbobi zuwa bil adama.

Dalili na 4: Sabuwar cutar coronavirus ba lallai ne ta kasance tana da alaka da dakin gwaje gwaje ba, a hakikanin gaskiya akwai yiwuwar gama garin mutane sun fi hadarin yiwuwar kamuwa da cutar sama da masana binciken kwayoyin cutuka. (Mai fassara: Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China