Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Steve Bannon na hura wuta
2020-05-03 21:39:19        cri

Kwanan nan, a yayin da Steve Bannon, mai tsattsauran ra'ayin siyasa na kasar Amurka ke zantawa da menama labarai, ya shafawa kasar Sin kashin kaji bisa ga matakanta na dakile cutar COVID-19, har ma a cewarsa, ya kamata kasar Sin ta biya hasarorin tattalin arzikin da aka sha sakamakon yaduwar cutar.

Kasancewarsa tsohon babban mashawarcin kasar Amurka, Steve Bannon yana rike da tsattsauran ra'ayin siyasa, kuma kullum yana son hura wutar kiyayya da juna da kuma yayata manufar wariyar launin fata. Ga shi a wannan karo, yaduwar cutar COVID-19 ta ba shi damar yayata manufarsa.

Sai dai karyarsa ba ta iya canza gaskiyar lamarin ba. Tun bayan barkewar cutar, kasar Sin ta sanar da hukumar lafiya ta duniya WHO kan yanayin cutar ba tare da rufa-rufa ba, ta kuma bayyanawa kasashen duniya yanayin kwayar cutar yadda ya kamata, tare da aiwatar da hadin gwiwar yaki da cutar tare da masanan kasa da kasa. Har ma domin kare yaduwar cutar, ta rufe birnin Wuhan na kasar, matakin da ya haifar da nasarar a zo a gani.

Baya ga haka, zancen wai "biyan diyyar hasara" bai dace da ka'idar kasa da kasa ba. Tuni kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi nuni da cewa, da cutar H1N1 da ta barke a kasar Amurka a shekarar 2009 wadda daga bisani ta yadu zuwa kasashe da shiyyoyi 214, da cutar kanjamau da aka fara gano ta a shekarun 1980 a kasar ta Amurka, har kuma da matsalar hada-hadar kudi da ta afku a Amurka a shekarar 2008, wadda kuma ta shafi kasashen duniya, kasashen duniyar ba su bukaci Amurka ta biya su diyya ba, to, mene ne kuma dalilin da ya sa 'yan siyasa irin su Mr. Bannon za su bukaci kasar Sin ta "biya diyyar hasarar da aka yi"?

Har yanzu masanan ilmin kimiyya na kokarin gano asalin cutar, kuma 'yan Adam baki daya na fuskantar hasarar cutar. Abokin gaban kasar Amurka cuta ce, a maimakon kasar Sin.

Yanzu haka yawan mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar ya zarce miliyan 1.12 a kasar Amurka, a yayin da yawan mamata ya wuce dubu 66. A sa'i daya kuma, alkaluman GDP na kasar ya ragu da kaso 4.8% cikin farkon watanni uku na bana, raguwar da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan faruwar matsalar hada-hadar kudi a shekarar 2008. Sai dai abin takaici ne a duniya ke damuwa da yanayin cutar a kasar, wasu 'yan siyasar kasar na maida hankalinsu kan tada rikici da dora laifinsu kan kasar Sin a maimakon su hada karfinsu wajen shawo kan cutar, lamarin da ya bata lokacin ceton rayukan jama'a.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China