Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jama'ar kasar Sin jarumai ne wadanda ke ba da gudunmmawa ga aikin yakar COVID-19
2020-05-01 16:24:07        cri

Ranar 1 ga watan Mayu, rana ce da aka kebe domin jinjinawa ma'aikatan kasa da kasa. Sa'an nan yanayin fama da cutar COVID-19 da muke ciki ya sa ranar ma'aikata ta wannan karo samun wata ma'ana ta musamman.

Tun lokacin da aka samu barkewar annobar COVID-19 a nan kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya bayyana aikin dakile yaduwar cutar a matsayin "wani yaki da ya shafi dukkan jama'ar kasar", inda ya bukaci a dora matukar muhimmanci kan tsaro da lafiyar jama'a, gami da dogaro kan jama'a ta yadda za a samu cikakken karfin yaki da annobar.

Daga bisani, dubun-dubatar ma'aikata na kasar Sin sun yi iyakacin kokarin samar da kayayyaki da hidimomin da ake bukata don dakile yaduwar cutar, lamarin da ya ba kasar damar shawo kan cutar a cikin gidanta. Saboda haka, yayin da shugaba Xi yake zantawa da wani shugaban kasar waje, ya ce, jama'ar kasar Sin sun ba shi cikakken imani kan samun nasara a kokarin shawo kan cutar, don haka jama'ar kasar jarumai ne na gaske.

Hakika a wannan yakin da kasar Sin take yi da mummunar annoba ta COVID-19, kusan babu wani dan kasar da ya nade hannu ba tare da samar da wata gudunmmawa ba. Dukkan al'ummar kasar fiye da biliyan 1.4 suna taka rawar a zo a gani bisa mabambantan matsayinsu. Duk wanda ya ga yadda daidaikun Sinawa suke kokarin samar da nasu gudunmmawa ga aikin dakile yaduwar cutar COVID-19, to zai kara fahimtar dalilin da ya sa kasar ta iya samun nasara a wannan yaki da take yi da wata mummunar cuta mai matukar kisa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China