Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Laifuka Guda 4 Da Mike Pompeo Ya Aikata 
2020-04-28 20:10:39        cri
Hakika ba mu taba ganin wani sakataren harkokin wajen kasar Amurka da ya yi kama da Mike Pompeo ba, wanda yake daukar dabarun da ya saba yi na "karya, cuta, da sata" da ake yawan amfani da su a hukumar leken asiri ta CIA, sa'an nan ya ci gaba da aiwatar da su a fannin diplomasiyya, lamarin da ya zubar da kimar kasar Amurka a idanun duniya. Amma baya ga karerayin da Pompeo yake tafkawa da ba su ishe shi ba, har ma yana kokarin wuce gona da iri, inda abubuwan da yake aikata bayan barkewar cutar COVID-19 sun saba hankali matuka.

Dangane da laifukan da mista Pompeo ya aikata a wannan karo, Kurt Campbell, tsohon mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka, da Rush Doshi, wani shehun malami mai nazarin harkoki masu alaka da kasar Sin a jami'ar Yele ta kasar Amurka, sun rubuta a cikin wata makala cewa, za a iya kasa laifukan da shi Pompeo ya aikata zuwa fannoni guda 4.

Na farko, yadda ya katse tallafin da kasar Amurka ke samar wa hukumar lafiya ta duniya WHO wani babban laifi ne wanda zai lahanta kasashe masu koma bayan tattalin arziki, gami da gungun mutane masu rauni.

Na biyu, don neman boye rashin nasara da kasar Amurka ke samu a fannin dakile cutar COVID-19, mista Pompeo ya yi kokairn dora laifi ga kasar Sin, da ruruta kiyayya, da yin zagon kasa ga yunkurin kasashen duniya na yakar COVID-19 tare.

Na uku, duka da cewa, annobar ta riga ta haifar da illoli ga dan Adam, abin takaici shi ne, mista Pompeo na ci gaba da neman matsawa kasashen Iran, da Cuba lamba, lamarin da ya haddasa rasa rayuka da yawa a wadannan kasashen.

Sa'an nan na hudu, mista Mike Pompeo ya nade hannu ba tare da yin wani abu ba a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar Amurka, inda ya yi kokarin kare muradunsa a fannin siyasa, maimakon kula da lafiyar jama'ar kasarsa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China